Sana’o’i guda 13 na yi a rayuwata – Malam Muhammadu Buhari

Me ne tarihin ka? Asalina Bagobiri ne amma mahaifiyata Bakatsina ce, garinmu shi ne kagal da ke Kudancin garin Fegi da ke karamar Hukumar Batsarin Jihar Katsina. Shekaruna 63, an tura ni karatun allo a kasar ‘Yanduna da ke karkashin Sandamu da ke masauratra Daura. Mun sha wahalar ruwa, don wani wurin sai an sa […]

Sana’o’i guda 13 na yi a rayuwata – Malam Muhammadu Buhari

Me ne tarihin ka?

Asalina Bagobiri ne amma mahaifiyata Bakatsina ce, garinmu shi ne kagal da ke Kudancin garin Fegi da ke karamar Hukumar Batsarin Jihar Katsina. Shekaruna 63, an tura ni karatun allo a kasar ‘Yanduna da ke karkashin Sandamu da ke masauratra Daura. Mun sha wahalar ruwa, don wani wurin sai an sa Jakai su janyo ruwa a rijiyar mai gaba 20, kuma kwakware biyu kadai ake da su a garin da ke da gida fiye da tamanin. Ina dan shekara goma sha daya aka kai ni. A lokacin ana yi wa Daura kirari da cewa, “Kana shan ruwan taro ba ka koshi ba”

Me ya sa ka bar makarantar allo? 

Wani yaro ne dan makarantarmu ya je gidan da nake musu aikatau suna ban abinci da yamma ya ce a ba shi abincina don ni ba zan zo ba. Sun cinye ke nan tare da sauran yara sai na iso, da na ga haka sai na jira uban gidana ya rage abinci, da aka ba mu sai ya mika min dunkulen kasa a madadin loma don da duhu, sai na jefe shi da dutse, sai ya fadi ya ce na karya masa baya, sai yara suka ce za su buge ni domin mahaifinsa na kusa da Malaminmu ne don haka in ya fada wa mahainfinsa, zai fada wa malam a buge ni domin yaron dan gata ne. Washegari za a tafi gona sai na gudu.  Daga nan na yi sana’o’i da yawa kamar tallar kuli da fasa dutse da tallar biredi, da yaron mota da gadi da lodin yashi da gyaran takalmi da sayar da lemu da ayaba  da gini  da aikin tireda  da dillanci da kuma aikin gidan bulo.  

 Yaruka nawa ka ke ji?

Ina ji ko kuma fahimtar Hausa, Fulatanci, Yarbanci, Turanci da kuma Inyamuranci.