Sanarwar hari kan Ukraine: Jawabi biyu, shiga daya
Kayan da Putin ya saka ranar Litinin sun yi kama da wadanda ya saka ranar Alhamis
Manazarta sun lura cewa shigar da Shugaba Vladimir Putin na Rahsa ya yi lokacin da ya ayyana yaki a kan Ukraine ranar Alhamis ta nuna cewa akwai yiwuwar nadar jawabin aka yi – ma’ana ba ranar ya yi jawabin ba.
A jawabin na ranar Alhamis – wanda aka yada ta talabijin da sanyin Safiya a Rasha – Mista Putin ya ce zai dauki “matakin soji na musamman” a kan Ukraine.
- Abu 10 Da Ya Kamata Ku Sani Kan Dokar Zaben Da Buhari Ya Sawa Hannu
- Attajiran Rasha Sun Yi Asarar Dala 39 bn A Rana Daya
Yayin wani jawabi da ya yi ranar Litinin ma, alamu sun nuna cewa wadannan kayan da ya yi jawabin Alhamis din da su ne a jikinsa.
A jawabin ranar Litinin din dai, Putin ya yi kakkausar suka a kan ’yancin Ukraine, yana cewa Tarayyar Soviet ce ta samar da ita.
A duka hotunan bidiyon biyu ga alama Putin ya zauna ne a wuri guda a kan teburi guda, yana sanye da kaya guda: wata bakar kwat da farar shat da kuma lektaye mai ruwan malmo.
Yaushe aka nada?
Wannan ne ya sa ake ta hasashen cewa ba kai-tsaye ya sanar da kaddamar da harin ba.
Wasu manazarta sun ambaci bayanai game da wani bidiyo daga hukumomi a matsayin hujjar cewa nadar jawabin aka yi.
Amma Aric Toler, wani manazarci mai aiki da kafar Bellingcat, ya ce bayanan daga wani bidiyon ne na daban.
Ya kara da cewa bayanan da suka fito daga Fadar Kremlin game da bidiyon sun nuna cewa ranar 24 ga watan Fabrairu aka nadi jawabin, lamarin da ya jefa shakku game da hakikanin lokacin da aka dauki sanarwar.