Sanata Abdallah Wali ya raba wa ’yan PDP shinkafar azumi

Sanata Abdallah Wali wanda ke neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a karkashin jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa ya raba wa ’yan jam’iyyar buhuhunan shinkafa dubu shida da 300 da kudinsu ya haura Naira miliyan 59.Sanata Wali ya shaida wa magoya bayan jam’iyyar a ofishin yakin neman zabensa cewa ya raba musu shinkafar ce […]

Sanata Abdallah Wali ya raba wa ’yan PDP shinkafar azumi
Sanata Abdallah Wali ya raba wa ’yan PDP shinkafar azumi

Sanata Abdallah Wali wanda ke neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a karkashin jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa ya raba wa ’yan jam’iyyar buhuhunan shinkafa dubu shida da 300 da kudinsu ya haura Naira miliyan 59.
Sanata Wali ya shaida wa magoya bayan jam’iyyar a ofishin yakin neman zabensa cewa ya raba musu shinkafar ce saboda ganin watan azumi ya kama akwai bukatar kowane mutum ya samu sukunin gudanar da ibadarsa cikin lumana da jin dadi.
Ya ce kowace mazaba daga cikin mazabu 244 da ke jihar za a ba ta buhu 20, sai hedikwatar jam’iyya na kananan hukumomi 23 za su samu buhu 20 kowaccensu, sai sakatariyar jiha za su samu buhu 100, in da dattijan jam’iyya za su dauki ragowar.
Sanata Abdallah ya gode wa sababbin shugabani jam’iyyar da aka zaba inda ya yi kiran su yi adalci a cikin rabon shinkafar don ta kai ga talakawa.
Da farko shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Alhaji Ibrahim Milgoma ya gode wa Sanata Wali kan wannan hobbasa da ya yi ga mambobinsu, kuma ya yi kira ga sauran jagororin jam’iyyar su yi koyi da shi don ganin an taimaki jama’a ta yadda jam’iyyar za ta tsaya da kafafunta a tabbatar da gaske take yi za ta karbe mulki a shekararar 2015 daga Jam’iyyar APC a jihar.