…Sanata Ahmad Lawan ne muke so ya gaji Mark – Gwamna Gaidam

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya nuna cikakken goyon bayansa ga Shugaban Majalisar Dattawa da Sanata Ahmad Lawan daga Jihar ke yi, inda ya ce ya cancanci samun wannan matsayi don maye gurbin shugaban majalisar mai barin gado Sanata Dabid Mark. Gwamna Gaidam ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa Alhaji Abdullahi Bego a […]

…Sanata Ahmad Lawan ne muke so ya gaji Mark – Gwamna Gaidam
…Sanata Ahmad Lawan ne muke so ya gaji Mark – Gwamna Gaidam

Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya nuna cikakken goyon bayansa ga Shugaban Majalisar Dattawa da Sanata Ahmad Lawan daga Jihar ke yi, inda ya ce ya cancanci samun wannan matsayi don maye gurbin shugaban majalisar mai barin gado Sanata Dabid Mark.

Gwamna Gaidam ya bayyana haka ne ta bakin kakakinsa Alhaji Abdullahi Bego a Damaturu, inda ya ce Sanata Ahmad Lawan mutum ne da ya san kabli da ba’adin aikin majalisa kasancewar tunda kasar nan ta koma tafarkin dimokuradiyya a 1999 ake damawa da shi a majalisun kasa. Ya ce ya cancanci samun wannan kujera tunda a halin da ake ciki al’ummar kasar nan sun zabar wa kansu canji ganin sun sa jam’iyyar ceton al’umma ta APC a gaba.
Gwamna Gaidam ya kara da cewa abin farin ciki ne yadda sanatocin shiyyar Arewa maso Yamma suka fito tare da ’yan uwansu sanatocin da ke wasu shiyyoyin suka bada goyon bayansu ga neman wannan matsayi da Sanata Lawan ke yi na shugabancin Majalisar Dattawa, kuma sun yi haka ne saboda ganin ya dace ya shugabanci majalisar sakamakon kwarewa da hazakar da yake da ita don ciyar da kasa gaba musamman a wannan lokaci.
Gwamnan ya nemi wakilan shiyyar Arewa maso Gabas a Majalisar Dattawa su jajirce don ci gaba da mara baya ga takarar Sanata Ahmad Lawan har sai an kai ga gaci.