Sanata Ahmed Aruwa ya rasu

Allah Ya yi wa Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Ahmed Aruwa rasuwa da safiyar yau Lahadi. Aruwa ya rasu da misalin karfe 4:30 na asubah a wani asibiti mai zaman kansa da ke unguwar Barnawa a jihar Kaduna. Dan uwan Aruwa, Suleiman Kuta ne ya tabbatar wa majiyarmu rasuwar tsohon Sanatan. Aruwa wanda ya […]

Sanata Ahmed Aruwa ya rasu

Allah Ya yi wa Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Ahmed Aruwa rasuwa da safiyar yau Lahadi.

Aruwa ya rasu da misalin karfe 4:30 na asubah a wani asibiti mai zaman kansa da ke unguwar Barnawa a jihar Kaduna.

Dan uwan Aruwa, Suleiman Kuta ne ya tabbatar wa majiyarmu rasuwar tsohon Sanatan.

Aruwa wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 1999 zuwa 2007, ya rasu ne bayan doguwar jinya.

Allah ya ji kansa da rahama, Amin.