Sanata Ali Wakili ya raba kayayyakin koyon sana’a ga matasa 100

  Shugaban Kwamitin Yaki da Talauci a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Wakili yaraba kayayyakin koyon sana’a  da suka hada da na nau’rorin Kwamfuta da kayan aikin walda ga matasa 100 da ya dauki nauyin ba su horo kan sana’o’in a wani yunkuri da ya yi na sama musu hanyar dogaro da kai. Matasan 56 daga […]

Sanata Ali Wakili ya raba kayayyakin koyon sana’a ga matasa 100
Sanata Ali Wakili ya raba kayayyakin koyon sana’a ga matasa 100

 

Shugaban Kwamitin Yaki da Talauci a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Wakili yaraba kayayyakin koyon sana’a  da suka hada da na nau’rorin Kwamfuta da kayan aikin walda ga matasa 100 da ya dauki nauyin ba su horo kan sana’o’in a wani yunkuri da ya yi na sama musu hanyar dogaro da kai.

Matasan 56 daga cikinsu sun samu horo ne kan aikin da na’urar Kwamfuta a Hukumar Samar da Aikin yi ta kasa (NDE0 , yayin da 44 suka samu horo kan aikin walda a Cibiyar Koyar da Fasahar Sufuri ta kasa (ITT) da ke Zariya, inda ake sa ran matasan za su kakkafa kananan masana’antu da kayayyakin tallafin da suka samu daga hannun Sanatan.

Da yake mika kayayyakin a garin Bauchi, Malam Ali Wakili ya ce wannan yunkuri yana daga cikin ayyukan da ya yi a mazabarsa na shekarar 2016.  Ya ce kawar da talauci ta hanyar koyar da sana’o’i ita ce babbar hanyar kawar da talauci mafi dacewa.

Sanata Wakili ya bukaci matasan su yi kyakkyawar amfani da kayayyakin domin kyautata rayuwarsu da ta iyalansu, sannan ya bai wa mutanen mazabarsa tabbacin cewa zai ci gaba da yin ayyukan da za su inganta rayuwar al’umma.

Darakta Janar a Hukumar NDE, Dokta Muhammad Ladan Argungu ya yaba wa Sanata Wakili saboda yadda yake aiwatar da ayyukan da dubban mutane za su amfana ta hanyar kakkafa kananan masana’antu da jama’a za su yi sana’o’in da za su bunkasa rayuwarsu kuma su kawo walwala da ci gaban tattalin arziki.

Dokta Ladan Argungu wanda Mataimakin Daraktan Sashen Koyon Sana’o’i na  Hukumar Malam Aliyu Abubakar ya wakilce shi ya ce fiye da shekara talatin da suka wuce matsalar talauci da rashin ayyukan yi suka sa hukumar ta zama babban bangon da ke tallafa wa kokarin da Gwamnatin Tarayya take yi domin yakar talauci da rashin aikin yi.

Shi kuwa Daraktan Cibiyar ITT, Dokta Aminu Musa Yusuf wanda Dokta Bayero Fara, Daraktan Bayar da Horo na Cibiyar ya wakilta ya ce wannan yunkuri da Sanata Wakili ya yi yazo a daidai lokaci, idan aka yi la’akari da matsalar rashin aikin yi da ta yi katutu a kasar nan.

Ya ce sana’a babban lamari ne da ke taimakawa wajen gina kasa da rage aikata miyagun laifuffuka da yakar talauci kuma ta rage rashin aikin yi. Ya bai wa Sanatan tabbacin cewa a shirye makarantar take ta yi hadin gwiwa da shi domin ci gaba da bayar da horo mai nagarta ga matasa. Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin su yi amfani da abin da suka koya, kuma su kula da kayayyakin da aka ba su.