Sanata Aliero ya raba kayayyakin more rayuwa ga al’ummar mazabarsa
Sanata mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattawa, Sanata Muhammadu Adamu Aliero ya rabawa al’ummar mazabarsa kayayyakin more rayuwa domin bunkasa tattalin arzikin al’ummar yankin nasa. Tun da farko da yake jawabi, Sanata Muhammad Adamu Aliero ya ce ya gina dakunan karatu guda uku a kowace karamar hukumar da yake wakilta. Ya kuma […]

Sanata mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattawa, Sanata Muhammadu Adamu Aliero ya rabawa al’ummar mazabarsa kayayyakin more rayuwa domin bunkasa tattalin arzikin al’ummar yankin nasa. Tun da farko da yake jawabi, Sanata Muhammad Adamu Aliero ya ce ya gina dakunan karatu guda uku a kowace karamar hukumar da yake wakilta. Ya kuma gina dakunan shan magani guda biyar a cikin kananan hukumomi 8 da yake wakilta.
Sanata Aliero ya ce, a yau kuma ya raba kayayyaki da suka hada da motoci guda 8 kirar fijo 406 wadanda aka ba shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomin da yake wakilta da kuma mashina guda 250 ga matasa, sai kuma injinan nika guda 560 wadanda aka ba mata, da kekunan dunki guda 500 wadanda aka ba mata matasa da injinan ban-ruwa guda 300 ga masu noman rani, ya kuma ba mata 2,000 kowace mace an bata Naira Dubu 10 domin yin kananan sana’o’i domin dogaro da kansu.
Haka kuma Sanatan ba nan kadai ya tsaya ba, ya ce a cikin wannan shekara ta 2018 hukumar bada ilimin furamare ta tarayya (UBE) za ta gina dakunan karatu guda 25 a kowace karamar hukuma a mazabarsa bisa hadin gwiwa da shi kansa.
Yayin da yake karbar kayayyakin da aka raba wa al’ummar mazabar, mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na mazabar Kebbi ta Tsakiya, Alhaji Ibrahim Maikwanoni Koko, ya ce al’ummar Kebbi ta Tsakiya sun ji dadi kwarai da gaske kuma wannan ya nuna cewa lalle ba su yi zaben tumun dare ba, kuma ya yi kira ga wadanda suka karbi wadannan kayayyaki da su yi kokari su yi amfani da su yadda ya kamata domin dogaro da kansu da na iyalansu.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu ya yaba game da namijin kokari da Sanata Adamu Aliero ya yi ga al’ummar wannan mazaba tashi, ya kuma yaba game da dimbin ayyukan da ya gudanar tun lokacin da yake majalisar Dattijai, kuma wannan ba karamin aikinsa ba ne, kowa ya san wanene Adamu Aliero a wannan kasa ba sai an fadi abin da ya yi wa mazabarsa ba, ya yi wa al’ummar Najeriya ma balle mazabarsa.