Sanata Alkali ya yi watsi da yarjejeniyar tsayar da ’yan takara APC a Gombe
Tsohon Ministan Sufuri, Sanata Saidu Ahmed Alkali, ya ki amincewa da zabin ’yan takara ta hanyar yarjejeniya da shugabannin jam’iyyar APC suka gabatar a Jihar Gombe.
Tsohon Ministan Sufuri, Sanata Saidu Ahmed Alkali, ya ki amincewa da zabin ’yan takara ta hanyar yarjejeniya da shugabannin jam’iyyar APC suka gabatar a Jihar Gombe.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Umar Alkali Jibril, ya fitar, Sanata Alkali wanda ke neman takarar gwamna a APC, ya ce tsarin yarjejeniyar ba shi da tushe a dimokuradiyya, kuma ya saba wa dokar zabe ta 2026.
Ya jaddada cewa Sashe na 84 (1) na dokar zabe ya wajabta jam’iyya ta gudanar da zaben fid-da-gwani ga dukkan mukaman zabe tare da kulawar INEC. Haka kuma, dokar ta amince da tsarin yarjejeniya ne kawai idan dukkan ’yan takara da aka tantance sun amince da rubutaccen janyewa daga takara.
Jibril ya ce yadda aka gudanar da tsarin yarjejeniyar a Gombe ya saba wa dokar zabe da kuma manufar gina dimokuradiyya ta cikin gida mai dorewa.
- 2027: Lissafin siyasa ya sauya bayan Obi da Kwankwaso suka koma NDC
- Pantami zai je kotu bayan APC ta ba Jamilu Gwamna takarar Gwamnan Gombe
- ’Yan bindiga sun sa wa mamona harajin N10m a Katsina
Sanarwar ta kara da cewa Sanata Alkali ya riga ya nuna jajircewarsa ta hanyar sayen fom din sha’awa da na tsayawa takara, wanda hakan ya tabbatar da matsayinsa a matsayin dan takara da ya dace a yi la’akari da shi.
Ya bayyana cewa tsarin yarjejeniyar ba zai taba yin tasiri ba, sai dai idan jam’iyyar ta koma ga zaben fidda gwani kai tsaye kamar yadda dokar ta tanada.
Saboda haka, Sanata Alkali ya bayyana cewa ya fice daga tsarin yarjejeniyar, wanda ya ce ba shi da tushe na kundin tsarin mulki ko na doka.
Duk da haka, ya tabbatar wa shugabannin jam’iyya da cikakkiyar biyayyarsa wajen ganin nasarar jam’iyyar a zaben 2027, tare da jaddada cewa zai yi amfani da dukkan hanyoyin da dokar zabe da kundin tsarin mulkin APC suka tanada wajen bayyana korafe-korafensa.