Sanata Bagudu ya raba buhunhunan shinkafa ga masu azumi

dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, Sanata Atiku Bagudu, ya raba kayan azumi ga al’ummar mazabarsa.Da yake raba kayan azumi a madadin Sanata Atiku Bagudu a Birnin Kebbi mai taimaka masa na musamman, Alhaji Abubakar Nayaya Birnin Kebbi ya ce Sanata Bagudu ya yi wannan kyauta ce ga marasa karfi, domin albarkacin wannan […]

Sanata Bagudu ya raba buhunhunan shinkafa ga masu azumi
Sanata Bagudu ya raba buhunhunan shinkafa ga masu azumi

dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, Sanata Atiku Bagudu, ya raba kayan azumi ga al’ummar mazabarsa.
Da yake raba kayan azumi a madadin Sanata Atiku Bagudu a Birnin Kebbi mai taimaka masa na musamman, Alhaji Abubakar Nayaya Birnin Kebbi ya ce Sanata Bagudu ya yi wannan kyauta ce ga marasa karfi, domin albarkacin wannan wata mai alfarma.
Alhaji Abubakar Nayaya ya yi kira ga al’ummar Musulmi su bi koyarwar da ke cikin watan azumi da kuma koyarwar Alkur’ani Mai girma, don ci gajiyar wannan wata mai alfarma.
Ya ce Sanata Bagudu ya raba shinkafa da kudi ga jama’a, inda kuma ya ba kananan hukumomin jihar 21 tirela goma na shinkafa domin raba wa jama’ar Musulmi ya kuma ba kungiyoyin sa-kai da na gwamnati.
Sanata Bagudu ya bukaci Musulmi su yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa kasa addu’a ganin halin da ta tsinci kanta na rashin tsaro. Ya ce babu wata kasa da za ta samu ci gaba matukar al’ummar kasar ba su zaune lafiya.