Sanata Barau ya kai ziyarar ta’aziyya a Kano

Sanatan ya kai ziyara daban-daban a jihar domin jajanta wa iyalan waɗanda aka yi wa rashi.

Sanata Barau ya kai ziyarar ta’aziyya a Kano

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Sanata Aminu Inuwa a ranar Lahadi.

Marigayi Sanata Inuwa, wanda ya wakilci Kano ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar Social SDP a Jamhuriyya ta uku, ya rasu ranar Juma’a.

Barau, ya yi addu’ar Allah Ya jiƙansa, sannan ya bayyana shi a matsayin dattijo mai daraja wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen bautawa Allah.

Barau, ya kuma kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan wasu abokan siyasarsa guda huɗu.

Ya ziyarci gidan mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Hon. Yusuf Aliyu Tumfafi, da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni, domin yi masa ta’aziyya kan rasuwar ɗan uwansa.

Daga nan, ya ziyarci, tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Balarabe Saidu Gani domin yi masa ta’aziyya kan rasuwar mahaifinsa, Alhaji Saidu Sale Gani.

A Ƙaramar Hukumar Birni, Barau ya yada zango a unguwar NNDC domin yi wa iyalan marigayi Alhaji Zubairu Dambatta ta’aziyya.

Marigayin ya kasance tsohon jami’i a Hukumar Tashar Ruwa ta Najeriya (NPA) wanda ya rasu yana da shekara 75.

Har ila yau, ya je Ƙaramar Hukumar Dala domin yin ta’aziyya ga Kwamared Alasan Uba Idris kan rasuwar yayarsa.

A yayin ziyarar, Barau ya yi addu’ar: “Allah Ya gafarta wa waɗanda suka rasu, Ya yafe musu kurakuransu.

“Ya kuma sa Aljannatul Firdausi ta zama makoma a gare su tare da bai wa iyalansu haƙurin rashinsu.”

Sanata Barau ya kai ziyarar ta’aziyya a Kano

Mun kusa kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya — Tinubu

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Gombe, ya rasu

Matatar Dangote ta rage farashin man fetur