Sanata Barau ya tura ɗalibai 70 karatu ƙasashen waje
Sanatan ya buƙaci ɗaliban su zama jakadu nagari a inda aka tura su karatu.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya tura ɗalibai 70 daga Jihar Kano zuwa ƙasashen waje don yin karatu a fannoni daban-daban.
Ɗaliban da aka zaɓa daga mazaɓu uku na Jihar Kano, sun tashi a ranar Lahadi a jirgin saman Ethiopian Airlines a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano.
- An kama matar da ke kai wa Bello Turji makamai a Zamfara
- Tinubu na ɓoye wa ’yan Najeriya gaskiyar halin da ƙasa ke ciki — Sule Lamido
A yayin taron bankwana da ɗaliban, Sanata Barau ya bai wa kowane ɗalibi kyautar dala 200, tare da sanar da gudunmawar naira miliyan 30 da sauran al’umma suka ba su.
Wannan shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarinsa na rage giɓin ilimi a Arewacin Najeriya tare da samar wa matasa ayyuka a manyan masana’antu.
Da yake magana a filin jirgin, Sanata Barau ya ce, “Ilimi shi ne mafita ga matsalolin da muke fuskanta a Arewacin Najeriya.
“Wannan shiri na tallafi yana ƙarawa ƙoƙarin gwamnati, musamman shirin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu kamar tsarin lamunin ɗalibai.
“Burina shi ne na bai wa waɗannan matasa damar samun ƙwarewa a fannoni masu muhimmanci kamar Artificial Intelligence da binciken zamani, domin su zama masu dogaro da kansu su kuma taimaka wajen ci gaban ƙasa.”
Tun da farko, an shirya wa ɗaliban taron bankwana a ranar Asabar, inda aka ba su takardun tafiya, kwamfutoci, aka bai wa mata Hijabi, da Alƙur’ani mai girma.
A jawabinsa ga ɗaliban, Sanata Barau ya buƙaci su mayar da hankali a kan karatunsu tare da zama jakadu na gari a Kano da Najeriya.
Ya ce, “An zaɓe ku ne bisa cancanta ba tare da la’akari da siyasa ko dangantaka ba. Ku mayar da hankali, sannan ku dawo domin tallafa wa jiharku da ƙasarku.”
Tallafin, wanda gidauniyar Barau I. Jibrin ta samar, na da nufin bai wa matasan Najeriya ilimi a fannonin ƙirƙire-ƙirƙire da ci gaba a ƙasar.