Sanata Bomoi ya janye daga takarar Gwamnan Yobe

A wani abu na ba zata Sanatan ya jaddada janyewarsa ne, duk da cewa tun farko ya tsayu kai da fata cewa sai dai a yi zaɓen fid-da-gwani.

Sanata Bomoi ya janye daga takarar Gwamnan Yobe

Sanata Mohammed Ibrahim Bomoi mai wakiltar Yobe ta Kudu kuma ya janye aniyarsa ta neman takarar gwamna a Jam’iyyar APC.

A wani abu na ba zata Sanatan ya jaddada janyewarsa ne, duk da cewa tun farko ya tsayu kai da fata cewa sai dai a yi zaɓen fid-da-gwani.

Bayan sanar da janyewarsa, ya kuma nuna amincewa da yarjejeniyar da Jam’iyyar APC ta amince da ita a Jihar Yobe.

Sanata Bomoi ya bayyana hakan ne a ranar Asabar bayan ganawa da Gwamna Mai Mala Buni a fadar gwamnati da ke Damaturu.

A cewarsa, jam’iyyarsu ta APC za ta ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai tare kuma da mayar da hankali kan ƙarfafa damarta kafin babban zaɓen 2027.

“APC ta ci gaba da kasancewa jam’iyya mai haɗin kai kuma ba za a iya raba ta ba, kuma za mu ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai da aiki don samun nasarar jam’iyyar bisa ga yarjejeniyar da ta cimma,” in ji Bomoi.

Da yake mayar da martani, Gwamna Buni ya yaba wa Sanatan saboda fahimtarsa, dattakunsa, da jajircewarsa ga haɗin kan jam’iyyar da ci-gaban jihar.

Gwamnan ya yi kira ga sauran ’yan takara a cikin jam’iyyar da su yi koyi da Sanata Bomoi ta hanyar fifita muradun jam’iyyar sama da burin ƙashin kai domin tunkarar zaven 2027 da haɗin kai.

Janyewar Sanata Ibrahim Bomoi daga wannan ƙudiri kan iya bayar da mamaki ga wasu al’ummomin jihar ta Yobe musamman ma mabiyansa da kuma su kan su al’ummar jihar waɗanda suke cewar ba su taɓa tsammanin zai janye cikin sauƙi haka ba.