Sanata Buruji da wasu ’yan majalisa sun rasa kujerunsu
Kotun sauraron koke-koken zaben ’yan majalisun jihohi da na tarayya, wadda ta yi zamanta a ranar Juma’ar makon jiya a unguwar Isabo a Abekuta, ta soke nasarar zaben ’yan jam’iyyar adawa ta PDP guda 7, ciki har da Sanata Buruji Kashamu, mai wakiltar Ogun ta gabas. Hakazalika, kotun ta soke zaben dan majalisar wakilai mai […]
Kotun sauraron koke-koken zaben ’yan majalisun jihohi da na tarayya, wadda ta yi zamanta a ranar Juma’ar makon jiya a unguwar Isabo a Abekuta, ta soke nasarar zaben ’yan jam’iyyar adawa ta PDP guda 7, ciki har da Sanata Buruji Kashamu, mai wakiltar Ogun ta gabas.
Hakazalika, kotun ta soke zaben dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Ijebu North da Ijebu South da Ogun water side, Adekoya Adesegun ta kuma soke zabukan ’yan majalisun jihohi guda 5, a inda ta ba da izinin sake zabe a yankin da abin ya shafa a cikin kwanaki 90.
’Yan majalisun jihohin sun hada da shugaban marasa rinjaye a majalisar Wale Alausa daga karamar Hukumar Ijebu-Ode, sai Odunta Rasak mai wakiltar Yewa North da Adejoun Oyenuga mai wakiltar Ijebu East sai Adebowale Ojo daga Ipokiya da Adebowale Solaja daga Ijebu North, wadanda dukkaninsu ’yan jam’ iyyar PDP ne.
dan takarar kujerar Sanata mai wakiltar Ogun East a jam’iyyar APC, Abiodun Adedapo ne ya garzaya kotun, inda ya kalubalanci nasarar da Buruji Kashamu ya yi a zaben da ya gabata, wanda shugaban kotun, Mai shari’a Tobei Eboire ya bayyana a matsayin mai cike da kura-kurai da arangizon kuri’u a kananan hukumomin 8 cikin 9 da aka yi zaben. Hakan ya sa ya soke zabukan kananan hukumomin 8, a inda ya ce karamar Hukumar Ijebu-Ode ce kadai aka yi ingantacen zabe, ya kuma ba da izinin sake yin sabon zabe a yankin da abin ya shafa cikin kwanaki 90.
Lauyar da ke kare Buruji Kashamu, Misis Ifioma Isonu ta ce, Sanatan tare da sauran ’yan takarar jam’iyyar PDP da suka rasa kujerunsu, ba su gamsu da shari’ar ba, domin haka za su daukaka kara a kotun koli.
Da yake mayar da martani a kan shari’ar, Buruji Kashamu ya ce ba daidai ba ne da kotun ta soke nasarar zaben nasa, domin kuwa har yanzu shi ke kan gaba da kuri’u 5,179. “Na tashi da kuri’u 75,856 shi kuma Dapo Abiodun yana da kuri’u 70,677, to mene ne gamin alkaluman da soke zaben? Ai abin da kotun ta ce shi ne, za a sake zabe a yankunan da abin ya shafa. Don haka har yanzu ni ne mai wakiltar Ogun ta gabas.” Inji shi.