Sanata Danbaba ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Sanatan ya kara da cewa manufofin jam’iyyar APC sun yi daidai da ra’ayinsa na kashin kansa.
Sanata Abdullahi Danbaba
Sanata Ibrahim Danbaba mai wakiltar Sakkwato ta Kudu ya sauya sheka daga babbar jam’iyyar hamayya ta PDP zuwa APC.
- ’Yan bindiga sun yi wa shugaban APC kisan gilla a Kaduna
- Maharan sun harbe shugabannin PDP biyu a Filato
Danbaba ya bayyana hakan a cikin wata wasika da ya rubuta wadda shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya karanta a zaman Majalisar na ranar Laraba.
Ya ce dalilinsa na barin jam’iyyar PDP shi ne irin rikice-rikicen da PDP ke fama da su a Jihar Sakkwato.
Sanatan ya kara da cewa manufofin jam’iyyar APC sun yi daidai da ra’ayinsa na kashin kansa.