Sanata Danso Sodangi ya riga mu gidan gaskiya

Sanata Sodangi ya rasu bayan shafe shekaru 70 a doron kasa.

Sanata Danso Sodangi ya riga mu gidan gaskiya

Sanata Abubakar Danso Sodangi

Tsohon wakilin Nasarawa ta Yamma a zauren Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Danso Sodangi ya riga mu gidan gaskiya.

Wata majiya daga danginsa, ta tabbatar da rasuwar Sanata Sodangi a zantawar da ta yi da wakilinmu ta wayar tarho daga birnin Lafiya na Jihar Nasarawa a ranar Litinin.

Majiyar wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce Sanatan ya rasu ne da tsakar dare wayewar garin yau Litinin a Babban Asibitin Garki da ke Abuja.

A cewarta, kafin rasuwarsa, marigayin ya yi fama da jinya da ta danganci ciwon koda.

Bayanai sun ce tsohon Sanatan ya rasu bayan shafe shekaru 70 a doron kasa.