Sanata Gaya ya zargi gwamnatin PDP da gazawa a kan tsaro
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya na mazabar Kudancin Kano a APC ya zargi Jam’iyyar PDP da gazawa wajen samar da tsaro da hana yawan kashe-kashen jama’a a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, inda ya yi kira ga masu zabe su canja gwamnatin PDP a zaben 2015.Sanata Gaya ya yi wannan tsokacin ne a yayin da […]
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya na mazabar Kudancin Kano a APC ya zargi Jam’iyyar PDP da gazawa wajen samar da tsaro da hana yawan kashe-kashen jama’a a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, inda ya yi kira ga masu zabe su canja gwamnatin PDP a zaben 2015.
Sanata Gaya ya yi wannan tsokacin ne a yayin da yake jawabi ga taron ’ya’yan tsohuwar Jam’iyyar ANPP a Kano, inda ya ce dimokuradiyya ta ba jama’a dama idan ba su gamsu da wata gwamnati ba, su canja ta da wata a zabe. Ya ce sanin kowa ne gwamnatin PDP ta gaza ba ’yan kasar nan tsaro. “Wa zai ce ya gamsu da yanayin tsaron da Gwamnatin Tarayya take bayarwa a yankin da yake fama da wadannan rigingimu? Idan kuwa har amsar ita ce ba a gamsu ba, ya kamata a nemi canji ta hanyar daukar mataki a zabe na gaba,” inji shi.
Ya ce sun yanke shawarar kin bin Shekarau ne lokacin da ya koma Jam’iyyar PDP saboda gamsuwar da suka yi cewa galibin ra’ayin jama’a ba ya tare da Shekarau ko PDP. Ya ce maimakon su bi son zuciyarsu ko kwadayin abin duniya, sun gwammace su kasance tare da ra’ayin jama’arsu.
Shi ma a nasa jawabin, tsohon dan takarar Shugaban kasa a tsohuwar Jam’iyyar NRC, Alhaji Bashir Othman Tofa ya ce sun shirya taron ne don su tabbatar wa jama’a cewa mafi yawan jama’a ba su bi Shekarau zuwa PDP ba, sabanin yadda mabiya Shekarau din ke yadawa.
Ya ce babu wadanda suka bi Shekarau sai masu kwadayin abin duniya kuma su ma ’yan tsiraru ne, a yayin da mafiya yawan ’ya’yan tsohuwar Jam’iyyar ANPP a jihar da daukacin kananan hukumomi 44 suna tare da su a Jam’iyyar APC.