Sanata Ida ya kai dauki ga makarantar firamare

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Sanata Ibrahim Ida ya hannanta ginin dakin na’ura mai kwakwalwa (Computer Center) mai dauke da na’urorin har 12 kyauta ga makarantar Furamaren dake Unguwar Abatuwa mallakar gwamnati wacce aka sanya sunasa ‘Sanata Ida Community Secondary School’.  Sanata Ida ya yi alkawalin gina wa wannan makaranta dakin kwanfuta din […]

Sanata Ida ya kai dauki ga makarantar firamare

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Sanata Ibrahim Ida ya hannanta ginin dakin na’ura mai kwakwalwa (Computer Center) mai dauke da na’urorin har 12 kyauta ga makarantar Furamaren dake Unguwar Abatuwa mallakar gwamnati wacce aka sanya sunasa ‘Sanata Ida Community Secondary School’. 

Sanata Ida ya yi alkawalin gina wa wannan makaranta dakin kwanfuta din ne a kwanakin baya, a lokacin bikin yaye dalibai da aka yi. Kazalika, bayan cika wasu alkawuran da ya yi a can baya wadanda suka hada da zagaye filin makarantar, gina wasu ajujuwa a matsayin gudunmuwa da sauran makamantansu. Har ila yau, Sanatan ya bayar da gudunmuwar kudi har naira milyan daya a matsayin mabudin asusun ajiya don tallafawa wannan makaranta wadda hukumar ilmi ta karamar hukumar ta sanyawa makarantar sunan shi, a shekarun baya bisa ga irin yadda yake taimakawa harkokin ilmi a Jihar Katsina baki daya.

A jawabinsa a wajen hannata dakin na’ura na milyoyin naira, Sanata Ida ya ce, ya yanke wannan shawara ne domin bayar da dama ga dalibai tun a matakin firamare da su shiga a cikin fagen koyon ilmi mai tafiya da zamani tare da zama wata zakaran gwaji a fadin jahar. Sannan ya yi kira ga masu hali a fadin jahar da su taimakawa ilmi duka na sashen biyu wato na addini da na boko domin haifar da matasa nagari. Kazalika, ya ja hankalin iyaye da cewa, su cigaba da baiwa yaransu ilmi musamman mata, maimakon aza masu talla wadda a karshe take kai su ga ayyukan assha. Sanata Ida ya kara yin kira ga gwamnatin jaha da ta taimaka ta ginawa makarantar bene domin samun ragowar cunkoson da ake samu a cikin aji. Sannan ya yi alkawarin gyaran fanfon burtsatsen da dan majalisa Sani Aliyu ya ginawa makarantar wanda har zuwa yanzu ba a fara amfani da shi ba saboda wasu ‘yan matsaloli. 

Da yake jawabin godiya, shugaban hukumar ilmin bai daya na jahar, Alhaji Lawal Buhari Daura ya ce, ba su da abin da za su bayyana na godiya akan irin wannan tallafi da Sanata Ida ke baiwa fannin ilmi da wasu abubuwan daban ba wai a cikin karamar hukumar Katsina ba, a fadin jihar baki daya. Kazalika shugaban hukumar ilmin ya yi alkawarin sanar da Mai Girma Gwamna Masari akan wannan roko da shi Sanatan ya yi na gina benaye a makarantar domin rage cunkoson daliban. 

daya daga cikin daliban da muka tuntuba ya ce, a da sai dai ya rika ganin hoton ita na’urar ko dai a cikin littafi ko kuma a shagon da ake yin aiki da ita. Amma yanzu ya san abin da ake kira kwamfuta kuma nan bada jimawa ba zai koyi aiki da ita. Haka kuma daliban makarantar sun gabatar da wake-waken nuna farin ciki tare da nuna godiyarsu ga wannan dakin kwamfuta da aka sanya wa suna “Hadiza Ibrahim Ida Computer Center”.