Sanata Idah yanzu ne nune ya haramta?
Bisa ga irin yadda guguwar siyasa take kadawa, musamman karatowar zabubbukan shekara mai zuwa a kasar nan, rahotanni sun tabbatar da cewa wasu `yan takarar neman mukamin gwamna a jihohin shiyyar Arewa maso Yamma da uwar jam`iyyar PDP ta tantance a Kaduna a farkon wannan makon, sun koka akan abin da suka kira karfa-karfa da […]
Bisa ga irin yadda guguwar siyasa take kadawa, musamman karatowar zabubbukan shekara mai zuwa a kasar nan, rahotanni sun tabbatar da cewa wasu `yan takarar neman mukamin gwamna a jihohin shiyyar Arewa maso Yamma da uwar jam`iyyar PDP ta tantance a Kaduna a farkon wannan makon, sun koka akan abin da suka kira karfa-karfa da neman mamaye kome da wasu gwamnonin jihohinsu suke yi a cikin wannan tafiya ta fitar da gwanayen da za su tsaya wa jam`iyyar a zabubbukan 2015 din, don haka suke neman lallai uwar jam`iyyar ta kasa ta sa baki, wajen ganin an yi kome cikin gaskiya da adalci, a kuma bisa ga tanade-tanaden tsarin mulkin da dokokin da jam`iyyyar ta shinfida, ko don jam`iyyar tasu ta samu kai bentanta a cikin zabubbukan.
Wasu daga cikin `yan takarar neman mukamin Gwamnan Jihohin Jigawa, Alhaji Abba Anas Adamu da Alhaji Ibrahim Aliyu tsohon mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi daga Jihar Kebbi, da kuma Sanata Ibrahim Idah daga Jihar Katsina. A cewar Kakinsu, Alhaji Ibrahim Aliyu sun shaida wa Manema labarai a Kaduna jim kadan bayan an kammala tantancesu, cewa, sun fahimci irin yadda gwamnoninsu suka yi uwa su ka yi makarbiya cikin kankane zabubbukan wakilai da irin yadda suka nuna dan takarar da suke so ya gaje su. Ya nuna shakkunsu na babu batun za su samu adalci a cikin zabubbukan fitar da gwanayen jam`iyyar masu zuwa, abin da suka ce ba abin da zai haifar sai dakushe zukatan `yan jam`iyya da magoya baya, abin da ka iya haddasa rashin samun nasarar jam`iyyarsu.
A can jihata ta Katsina ma irin wadannan labarai ake ta yamadidi da su a cikin jam`iyyar ta PDP, tun bayan da Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Shehu Shema ya yi nune akan Kwamishinansa na Ma`adanai Injiniya Musa Nashuni, a zaman wanda yake so ya gaje shi. Wasu da suke kiran kansu masu ruwa da tsaki a cikin jam`iyyar ta PDP, da sauran masu neman takarar gwamnan jihar a inuwar jam`iyyar su shida, suna can sun dukufa wajen ganin lallai Injiniya Nashunin bai kai labari ba. Rahotanni sun tabbatar da cewa masu neman takarar sun yi taro a Abuja, inda suka dauki matakan ganin sun dakile aniyar gwamnan. Shi kuwa Kwamitin Tuntuba da ke karkashin rikon tsohon Sufeto Janar na `Yan sandan kasar nan Alhaji Ibrahim Coomasie da Sakataren riko Alhaji Aliyu Sani da suka ce sun samu koken `yan takarar neman mukamin gwamnan jihar na PDP, bisa ga zargin da suka yi na Gwamna Shema ya mamaye komai, kira suka yi ga uwar jam`iyyar ta PDP ta kasa kan lallai ta duba wadannan koke-koken da aniyar ta yi masu adalci.
Manema labarai a Abuja sun kalato daga majiyar taron`yan takarar suna cewa idan Gwamna Shema yana son ya dauko wanda zai gaje shi, don dorawa akan ayyukan da ya yi daga cikin Kwamishinoninsa, to, akwai bukatar ya dauko Kwamishinan da ya ba da gudummuwa a ci gaban jam`iyya kuma sananne ga `yan jam`iyya, ba Injiniya Nashuni ba, da `yan jam`iyya ba su san shi ba, wanda kuma zai yi wuyar sayarwa a jihar.
Wani hanzarin da masu wancan ra`ayi suka kawo shi ne wai tsayar da Injiniya Nashunin a zaman gwamnan daga yankin Kankiya, zai juya tare da rikita tsarin raba mukaman siyasa da ake aiki da shi a jihar tun da aka fara mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999, wato a wannan karon za a yi mulki ba Masarautar Daura. Manema labarai sun tabbatar da cewa sun tuntubi Sanata Idah akan wancan taro na Abuja, inda ya tabbatar musu da an yi shi, amma kuma ya ki ya ce uffan akan wadannan matakai da suka dauka na kokarinsu na ganin Injiniya Nashuni bai kai labari ba.
Tarihin kafuwar Jihar Katsina da aka kirkiro a shekarar 1987, daga cikin tsohuwar Jihar Kaduna ya tabbatar da cewa kananan Hukumomi bakwai aka taho da su kamar haka:- Katsina da Mani da Malumfashi, da Daura da Funtuwa da Dutsin-Ma da Kankiya, wadannan kananan Hukumomi bakwai su suka haifi kananan Hukumomi 34, da ake da su yau a jihar. Dadin-dadawa tsofaffin kananan Hukumomin nan a yau da su aka yi ma`aunin fitar da `yan Majalisar Dattawa uku na jihar, wato Katsina ta tsakiya da ta kunshi tsofaffin kananan hukumomin Katsina da Dutsin-Ma. Sai Mazabar dan Majalisar Dattawa ta Katsina ta kudu da ta kunshi Funtuwa da Malumfashi, ya yin da tsofaffin kananan Hukumomin Mani da Daura da Kankiya suke da dayan dan Majisar Dattawan.
Tarihi ya tabbatar da cewa tunda aka fara harkokin dimokuradiyya ta jamhuriya ta uku da ba ta kai labari ba, wato daga 1991 zuwa 1993, mazabar Katsina ke samun mukamin gwamnan jihar (Alhaji Sa`idu Barda 1992 zuwa 1993, a inuwar jam`iyyar NRC). Da aka dawo wannan karon a inuwar jam`iyyar PDP, an samu marigayi Gwamna Alhaji Uamru Musa `Yar`aduwa (1999 zuwa 2003), sai Gwamna Ibrahim Shehu Shema (2003 zuwa yau), dukkansu daga mazabar Katsina ta tsakiya suke, yayin da dukkan mataimakansu daga mazabar Katsina ta kudu suke, wato Ambasada Abdullahi Garba Aminci da ya yi zamani biyu wato lokacin Gwamna Sa`idu Barda da kuma a zango na biyu na marigayi `Yar`aduwa. Sai Alhaji Tukur Jikamshi,wanda ya rufa wa `Yar`duwa baya a zangonsa na farko. Barista Surajo Damari shi ne mataimakin Gwamna Shema a zangonsa na farko, yanzu kuma ana danawa da Barista Abdullahi Garba Faskari.
Akan batun Kakakin Majalisar Dokoki kuwa na san cewa a zango na biyu ne kawai na `Yar`aduwa Masarautar Daura ba ta samu mukamin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina ba, kuma sama da kasa ba ta hade ba akan haka, hakan kuma bai hana PDP ta kasa cin zaben gwamna ba, karewa ma da karau a zabubbukan 2007, da Gwamna Shema ya shigo Sanata Injiniya Kanti Bello na mazabar dan Majalisar Dattawa ta Daura, ya canja sheka daga jam`iyyarsa ta ANPP, ya koma PDP ya kuma sake komawa kan kujerarsa. Don me sai yanzu su Sanata Idah ke binbinin PDP ba za ta ci zabe ba, idan an tsayar da Injiniya Nashuni da ya fito daga yankin na Daura. Ina Sanata Idah da ire-irensa suke lokacin da aka kawo wa Jihar Katsina Gwamna Shema a shekarar 2003. Na san Sanata Idah ba ya cikin wadanda suka kafa PDP a jihar Katsina bare a kasa baki daya, bai shigo PDP ba sai da ta zauna da giindinta, aka kuma yi nune akan sa, ya kuma yi nasara. Yanzu din ma da ya fadi a shekarar 2011, ai a Abuja inda suka fi wayo shi da ire-irensa suka tare, sai yanzu suka sadado ganin kaka ta yi suka zo su girbi amfanin gonar da ba a noma da su ba.
Daga yadda wannan jamhuriyar ta fara har kawo yanzu, ban ga batun wani ya bauta wa jam`iyya, ko an san shi don dadewa cikinta kana zai iya kai bentansa (a dukkan jam`iyyun kasar nan). Idan da wadannan hanzari da makamantansu suna da tasiri wajen dafa madafun iko a siyasar wannan zamanin da Cif Olusegun Obasanjo bai zama shugaban kasa ba, haka mutane irinsu Alhaji Umar Tanko Al-Makura da Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako da Malam Isah Yuguda na jihohin Nassarawa da Sakkwato da Bauchi bi-da-bi da basu zama gwamnonin jihohinsu ba.
Tunda dai masu ruwa da tsaki na jam`iyyar PDP, sun amince shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan shi ne dan takara daya tilo na jam`iyyarsu. Mene ne laifin gwamnonin jihohi in sun yi nune kuma sun zauna akan sa? Haba su Sanata Idah, sai yanzu nune ya zama Haram a jam`iyyarku ta PDP?