Sanata Isa Galaudu yana nan a PDP – Isah Mashaya

Wani na hannun daman Sanata Isa Galaudu da ke wakiltar Kebbi ta Arewa a karkashin Jam’iyyar PDP Alhaji Isah Mashaya Argungu ya ce har yanzu sanatan yana na daram a Jam’iyyar PDP.Alhaji Isah Argungu ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a Birnin Kebbi dangane da rade-radin cewa Alhaji Isa Galaudu na […]

Sanata Isa Galaudu yana nan a PDP – Isah Mashaya
Sanata Isa Galaudu yana nan a PDP – Isah Mashaya

Wani na hannun daman Sanata Isa Galaudu da ke wakiltar Kebbi ta Arewa a karkashin Jam’iyyar PDP Alhaji Isah Mashaya Argungu ya ce har yanzu sanatan yana na daram a Jam’iyyar PDP.
Alhaji Isah Argungu ya bayyana haka ne lokacin da suke tattaunawa da wakilinmu a Birnin Kebbi dangane da rade-radin cewa Alhaji Isa Galaudu na cikin sanatocin da suka bar Jam’iyyar PDP. “Wannan ba gaskiya ba ne illa dai maganganun mutane ne kawai, hasali ma a lokacin da aka fara yada wannan maganar Sanata Isa ba ya a cikin kasar nan ya ta fi Ingila wajen wani aiki, amma sai
kwatsam muka ji ana ta yawo da maganar wai Sanata ya bar Jam’iyyar PDP,” inji shi.
Alhaji Isah ya ci gaba da cewa Sanatan wanda al’umma suka yi tsaye suka zaba ba ya tunanin haka kawai zai yi gaban kansa ba tare da ya yi shawara da mutanensa ba.
Sannan rubutun da wadansu kafafen labara suka yada cewa suka yi wadanda ake sa ran za su bar PDP zuwa APC, ba wai sun bar PDP din ba ne.
Ya ce duk da yake an san wannan lokacin mulkin siyasa ne da ta ba kowa ’yancin fadin albarkacin bakinsa, amma mutane su guji yada abin da ba su da hakikanin gaskiyarsa.