Sanata Isaiah Balat ya rasu yana da shekara 61
Mai ba Shugaban kasa Shawara kan Ayyuka na Musamman a ofishin Mataimakin Shugaban kasa Sanata Isaiah Chawai Balat ya rasu a ranar Talatar da ta gabata a Asibitin kasa da ke Abuja, bayan gajeriyar jinya.Sanata Balat wanda ya rasu yana da shekara 61 ya rasu ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen kai shi kasar […]

Mai ba Shugaban kasa Shawara kan Ayyuka na Musamman a ofishin Mataimakin Shugaban kasa Sanata Isaiah Chawai Balat ya rasu a ranar Talatar da ta gabata a Asibitin kasa da ke Abuja, bayan gajeriyar jinya.
Sanata Balat wanda ya rasu yana da shekara 61 ya rasu ne a daidai lokacin da ake shirye-shiryen kai shi kasar Jamus don yi masa jinya, bayan kwantar da shi a Asibitin kasar.
Marigayin ya zama Minista a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje tsakanin Mayun 1999 zuwa Disamban 2000, sannan ya zama Sanatan Kaduna ta Kudu daga Mayun 2003 zuwa Mayun 2007. Sai kuma ya nemi tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kaduna inda Mataimakin Shugaban kasa Namadi Sambo ya kada shi a zaben fidda gwani a shekarar 2007.
An haifi Sanata Balat a kauyen Gora da ke karamar Hukumar Zangon Kataf da ke Jihar Kaduna, inda ya rasa mahaifiyarsa yana jariri, kuma renonsa ya koma hannun kakarsa har ya girma.
Bayan karatunsa na firamare da sakandare, Balat ya halarci kwas kan harkokin kasuwanci a Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Kaduna tsakanin 1976 zuwa 1978, sannan ya halarci kwas a Makarantar Harkokin Kasuwanci ta Harbard da kuma Kwalejin Harkokin Man Fetur da Makamashi ta Odford duk a kasar Ingila.
Ya kafa Gidauniyar Isaiah Balat Foundation domin gudanar da allurar rigakafin sankarau ga kimanin mutum miliyan daya a Jihar Kaduna. Ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya biyar.
Wani amininsa kuma tsohon Kantoman karamar Hukumar Lerer Mista Dogara Achayi, ya shaida wa Aminiya cewa yana fama da jinya a ’yan watannin da suka gabata, lamarin da ya sa ya bar mukamin minista ga Laurentia Laraba Mallam.
A gidansa da ke Gora Close a daf da Gora Road a Unguwar Rimi GRA, abokan siyasarsa sun hallara suna jimamin mutuwarsa, inda suke ta kiran wayoyin aminansa.
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Dabid Mark wanda ya zubar da hawaye lokacin da ya ji labarin rasuwar ya bayyana Balat da dan siyasa abin koyi gogaggen dan majalisa kuma dattijon da ake girmamawa.
Shugaban Majalisar Wakiali Alhaji Aminu Waziri Tambuwal a sakon ta’aziyyarsa ya bayyana mutuwar Balat a matsayin mai girgizawa, inda ya ce Balat wani “fitaccen dattijo ne.”