Sanata Lado ya ba da Naira Naira miliyan 20 ga jagororin PDP 4000 a Kano

dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Tsakiya Sanata Basheer Mohammed Lado ya bayar kyautar Naira dubu biyar-biyar ga jagororin PDP 4000 da ke Jihar Kano.Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sanatan da ke Abuja ta ce dan majalisar ya bayar da kudin ne lokacin da ya gana da sababbin shugabannin Jam’iyyar PDP daga […]

Sanata Lado ya ba da Naira Naira miliyan 20 ga jagororin PDP 4000 a Kano
Sanata Lado ya ba da Naira Naira miliyan 20 ga jagororin PDP 4000 a Kano

dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Tsakiya Sanata Basheer Mohammed Lado ya bayar kyautar Naira dubu biyar-biyar ga jagororin PDP 4000 da ke Jihar Kano.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sanatan da ke Abuja ta ce dan majalisar ya bayar da kudin ne lokacin da ya gana da sababbin shugabannin Jam’iyyar PDP daga kananan hukumomi 15 da mazabu 174 na Kano ta Tsakiya, inda jimillar kudin ya kama Naira miliyan 20.
Sanata Lado ya taya sababbin shugabannin PDP na mazabun unguwanni da kananan hukumomi da ke shiyyar, inda ya yi kiran su ci gaba da sadaukar da kai don samun nasarar jam’iyyar a zaben 2015 da ke tafe.
Ya ba su tabbacin cewa jam’iyyar za ta farfado a Jihar Kano, inda ta rasa kujerar Gwamna sakamakon ficewar Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso zuwa Jam’iyyar APC a farkon wannan shekara.
“Wannan ne farkon ganawa da ku. Kuma za mu ci gaba da ganawa a kai- a kai tare da karafafa dabaru kafin zabe wanda muke da tabbacin jam’iyyarmu za ta lashe,” inji Sanatan.
Ya ce gwamnatin PDP a matakin tarayya tana aiwatar da ayyuka na biliyoyin Naira a Jihar Kano ta hanyar ayyukan mazabunsa ciki har da gadar sama a cikin birnin Kano.
Da yake mayar da jawabi a madadin shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomin 15, Shugaban Jam’iyyar PDP na karamar Hukumar Kumbotso Garba Mai Zabi ya nanata kudirinsu na sadaukar da kai wajen samun nasarar jam’iyyar a zaben badi.
Mai Zabi ya ce Kano ta Tsakiya ba ta taba ganin kyakkyawan wakilci kamar yanzu ba, inda suka yi alkawarin kasancewa tare da Sanata Lado a inda ya nufa a harkokin siyasarsa.