Sanata Ladoja ya gargadi kabilar Ibo kan raba Najeriya
Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Rasheed Ladoja, ya mayar da martani ga wadansu ‘yan tsirarun kabilar Ibo da suke yunkurin ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Biyafara.Ya ce sashin Kudu maso gabas (na kabilun Ibo zalla) ba zai taba samuwa ba domin cin gashin kai shi kadai ba tare da Najeriya ba, domin kashi 70 […]
Tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Rasheed Ladoja, ya mayar da martani ga wadansu ‘yan tsirarun kabilar Ibo da suke yunkurin ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Biyafara.
Ya ce sashin Kudu maso gabas (na kabilun Ibo zalla) ba zai taba samuwa ba domin cin gashin kai shi kadai ba tare da Najeriya ba, domin kashi 70 daga cikin 100 na yawan kabilun Ibo sun warwatsu ne a sassa daban-daban na Najeriya. Sauran kashi 30 na wannan al’umma, su ne suke zaune a cikin gidajensu a sashen Kudu maso gabas.
Sanatan ya fadi haka ne ga ’yan jarida a ranar Juma’a a cikin gidansa da ke Ibadan, jim kadan bayan dawowa daga Sallar Idi. Ya ce, idan kabilun Ibo suka yi kuskuren ci gaba da yunkurin ballewa daga Najeriya to, kuwa a kansu wahalar za ta kare, domin mafi yawancin mutanen nasu sun bazu cikin kasa ne da ba za su iya komawa gida ba. Saboda haka ya kamata masu yin wannan yunkuri su mayar da akalarsu baya domin guje wa samun kansu cikin wahala. Ya ce bai dace Ibo su sake jefa Najeriya cikin wata matsala bayan irin wadda suka yi a shekarun baya da ba su yi nasara ba.
Ya kara da cewa, jami’an tsaron kasa sun yi daidai da suka toshe hanyoyin watsa labarai da tashar Rediyon Biyafara ke yin amfani da ita wajen isar da haramtaccen sako ga masu sauraro.
Dangane da masu hamayya da yawan korafi ga salon mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, sai tsohon gwamnan ya ce: “Lokaci bai yi ba da za a fara yin korafi ga Shugaba Buhari. Har yanzu bai riga ya cika kwanaki 100 daga cikin kwanaki 1500 a kan mulki ba. Mene ne dalilin da za a fara sukar mutumin da bai cika watanni 3 a kan mulki ba? Ba za ka taba tunanin mutumin da ya dade rabonsa da gwamnati ya iya gano hanyoyin mulki farat daya ba. Wannan mutumi ya taba yin wannan aiki a baya wanda yanzu yake bin komai a hankali. Ina tunanin bai kamata mu yi hanzari ba, kamata ya yi mu kyale shi ya tafiyar da al’amuransa yadda yake so, domin gano bakin zaren. Watanni 6 sun isa mu yanke hukuncin irin kamun ludayinsa, ya yi da kyau ko akasin haka. Na yarda cewa Shugaba Buhari, ya san abun da yake yi wanda sakamako zai tabbatar da hakan.”
Da yake magana a kan ziyarar da Shugaba Buhari ya kai zuwa Amurka, sai Sanata Ladoja ya ce akwai muhimman dalilai da suka sanya Shugaba Buhari amincewa da yin wannan ziyara. daya daga cikin dalilan shi ne neman taimakon Amurka domin yaki da ’yan ta’addan Boko Haram da ake cewa sun hade da Alkaeda da ISIS. “Ya kamata mu ba shugaban hadin kai da goyon baya wajen ganin ya aiwatar da komai yadda yake so.”