Ibrahim Mantu: Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa ya rasu
Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ibrahim Mantu ya rasu.
Allah Ya yi wa tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ibrahim Mantu rasuwa.
Iyalan Sanata Ibrahim Mantu, sun sanar cewa ya kwanta dama ne kafin wayewar garin Talata, a wani asibiti a Abuja, bayan fama da rashin lafiya.
Latsa nan domin sauraren ‘Yadda zabuwa dokar man fetur za ta shafi rayuwarku’:
- Ba ni da sha’awar zama Shugaban Kasa — Sarki Sanusi
- Ahmed Joda: Tsohon Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya ya rasu
Majiyar ta ce kafin ko kafin a kai shi asibiti, Sanata Mantu ya yi jinya a gida, amma da abin ya yi tsanani sai aka dauke shi zuwa asibiti, a nan rai ya yi halinsa.
Iyalan sun ce nan gaba za a sanar da shirye-shiryen fitaccen dan siyasar kuma jigo a jam’iyyar PDP kuma dan kasuwa.
Sanata Ibrahim Mantu wanda dan asalin kauyen Chanso a Karamar Hukumar Gindiri ne a Jihar Filato, ya rike kujerar Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar Dattawa daga 1999 zuwa 2001.
A shekarar 2001 kuma aka zabe shi ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa daga 2001 zuwa 2007, lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ta shekarar 1999 zuwa 2007.
An haifa Sanata Ibrahim Nasiru Mantu ne a kauyen Chanso a ranar 16 ga Fabraitu, 1947, kuma ya yi karatun Digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Washington ta kasar Amurka.
Ya yi aiki a kamfanonin da ma’aikatu da dama kafin ya shiga siyasa a shekarar 1978.
Ya rasu kwana hudu bayan rasuwar Ahmed Joda, tsohon Babban Sakatare a Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Kwamitin Mika Mulki ga Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015.