Sanata Misau da ‘yan sanda sun sa zare

Bayan daukar lokaci ana musayar kalamai tsakanin rundunar ‘yan sanda da kuma Sanata Isah Hamma Misau, mai wakiltar shiyyar Bauchi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, rundunar ta ayyana cewa ta na neman sanatan ruwa a jallo domin amsa tambayoyi akan laifuka da dama.  Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, CSP Jimoh Mashood ne ya […]

Sanata Misau da ‘yan sanda sun sa zare

Bayan daukar lokaci ana musayar kalamai tsakanin rundunar ‘yan sanda da kuma Sanata Isah Hamma Misau, mai wakiltar shiyyar Bauchi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, rundunar ta ayyana cewa ta na neman sanatan ruwa a jallo domin amsa tambayoyi akan laifuka da dama. 

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, CSP Jimoh Mashood ne ya sanar da wannan hukuncin da rundunar ta yanke, ya na mai cewa har yanzu sunan sa na nan daram cikin jerin sunayen jami’an rundunar ‘yan sandan kasar nan.

Ya kuma ce Sanata Isa Misau ya zargi shugaban rundunar ‘yan sanda da karbar cin hanci kafin tura kwamishinoni zuwa jihohin da aka fi samun alherin ofis, tare da karkatar da wasu kudaden kimanin naira biliyan 10 duk wata, da yake karba daga wasu kamfanonin dake amfani da ‘yan sanda zuwa aljihunsa maimakon lalitar gwamnati.

Mashood ya kuma ce wannan zargi na Sanata Misau labarin kanzon kurege ne kawai, inda ya ce haka kawai sanatan ya daina zuwa aiki tun a ranar 24 ga Watan Satumbar 2010, sakamakon canjin wurin aikin da aka yi masa, wadda bai yi ma sa dadi ba.

Ya kuma kara da cewa takardar barin aikin da dan majalisar ya nuna ga manema labarai su a wurin su ta jabu ce. Rundunar ta kuma ce ta na neman sanatan ne ruwa a jallo don ya zo ya yi mata bayani dalla-dalla kan dalilin da ya sanya ya daina zuwa aiki ba tare da wani kwakwaran dalili ba.

Sai dai da yake mai da martini, Sanata Isa Hamman Misau ya ce shi bai gudu ba, yana nan kamar yadda rundunar ‘yan sandan ke zargi, ya na mai cewa rundunar ta na kokarin karkatar da hankulan al’ummar Najeriya ne daga abinda ake zarginta da shi. Inda ya ce idan bah aka ba me ya kawo maganar cewa har yanzu shi dan sanda ne, bayan da ya cike ka’idojin ajiye aiki tun a shekarar 2010, kuma ya biya hukumar kula da ‘yan sanda kudin barin aiki wajen sadaukar da albashinsa na wata guda akan naira dubu 120 a lokacin da ya bar aikin.

A farkon wannan makon ne dai wannan takaddama ta barke tsakanin bangarorin biyu, bayan da Sanata Misau ya zargi rundunar ‘yan sandan da karbar na goro kafin yi wa wasu daga cikin jami’anta karin girma tare da handame makudan kudade daga manyan kamfanonin man fetir.

Sanata Hamman Misau ya zargi Babban Jami’in ‘Yan Sandan, Ibrahim Kpotun Idris bisa tattara kimanin naira biliyan 120 don biyan kudin tsaro. Inda ya ce irin wannan aikin tsaro ne da ake yi wa kamfanoni, bankuna da kamfanonin man fetur da mutane da yawa a kowace shekara a duk fadin kasar, amma maimakon kudin su shiga aljihun gwamnati don karin kudin shiga, sai shugaban ‘yan sandan ya azurta kansa.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, Misau ya ce ana tura jami’an tsaron wurare masu tsoka ne kawai idan sun biya cin hanci. sai a kai ka ma’aikatar man fetur, ko guraren manyan mutane.

Ya kuma kara da cewa hatta canjin aiki da ake yi wa kwamishinonin ‘yan sanda da manyan kwamandojin mobayel, sai sun bada cin hanci sannan za ayi masu, kuma ba kananan kudi aka karba ba, kudi ne daga naira miliyan 10 zuwa 15.

Da farko dai sanatan ya yi ikirarin cewa a matsayinsa na tsohon jami’in rundunar ya samu korafe-korafe daga manya da kananan jami’an ‘yan sanda wadanda suka yi zargin cewa sai mai uwa a gindin murhu ko kuwa wanda aljihunsa ke cike da naira ake yi wa karin girma, inda ya bayyana cewa ana karbar kimanin naira miliyoyin kudi a wurin jami’an ‘yan sanda da ke bukatar karin girman.