Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio

Akpabio ya yi zargin cewa “ba ta san komai ba game da zaman majalisa…da kuma saka tufafi masu shara-shara.”

Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio

Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da ƙara a kotu tana ƙalubalantar shugaban majalisar, Godswil Akpabio, kan zargin ɓata mata suna.

Natasha ta shigar da ƙarar ne gaban Babbar Kotun Tarayya a ranar Talata, tana mai ƙarar Akpabio da babban mai taimaka masa Mfon Patrick.

Ta nemi Kotun Tarayyar da ta umarci waɗanda ake karar su biya ta diyyar naira biliyan 100 kan zargin ɓata mata suna, sannan a biya ta naira miliyan 300 a matsayin kuɗin shigar da ƙara.

Akpoti, wadda lauyanta Victor Giwa ya shigar da ƙarar a madadinta, ya yi ƙorafi kan kalaman da babban mai taimaka wa Shugaban Majalisar Dattawan ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Ta nemi kotun ta tilasta wa mutanen janye kalaman, sannan su nemi afuwarta a wani shafin jarida.

Ta ɗora zargin nata ne kan wani saƙo da ta ce Mista Patrick ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya soke ta cewa “ba ta san komai ba game da zaman majalisa…da kuma saka tufafi masu shara-shara.”

Barista Giwa ya yi zargin cewar kalaman ba komai ba ne illa, ɓata suna, da takalar faɗa, da ƙanskantar da ita a idon abokan aikinta, da sauran al’umma.

Sanata Natasha ta buƙaci kotun da ta haramta wa waɗanda ake ƙara ko makusantansa daga wallafa duk wani rubutu na ɓatanci a game da ita.

A makon da ya gabata ne Sanata Natasha Akpoti Uduaghan ta bayyana damuwa kan yadda aka bai wa wani ɗan majalisa wurin zamanta, saboda wasu sauye-sauye da aka yi a tsarin zaman majalisar.

Sanatar ta ƙi amincewa da sauyin wajen zaman da aka yi mata, wanda hakan ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin ta da Akpabio.

Lamarin na zuwa ne yayin da aka umarci kwamitin ladabtarwa na Majalisar Dattawan da ya gayyaci Sanata Natasha don bin bahasi kan rikicin sauyin wajen zaman.

A bayan nan ne aka yi zazzafar musayar yawu tsakanin Sanata Natasha da Akpabio kan sauya mata wurin zaman da ta ce an yi ba tare da amincewarta ba.