Sanata Ndume ya kalubalanci Gwamnati kan lalacewar tsaro
dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu Sanata Muhammad Ali Ndume, ya kalubalanci Gwamnatin Tarayya kan yadda take rikon harkar tsaro a yankin Arewa maso Gabas. Sanata Ali Ndume, ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da wakilinmu a Maiduguri, inda ya ce harkar tsaro ta tabarbare a yankin ta yadda baya […]
dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Borno ta Kudu Sanata Muhammad Ali Ndume, ya kalubalanci Gwamnatin Tarayya kan yadda take rikon harkar tsaro a yankin Arewa maso Gabas. Sanata Ali Ndume, ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da wakilinmu a Maiduguri, inda ya ce harkar tsaro ta tabarbare a yankin ta yadda baya ga kashe mutane da ake yi
akwai kuma batun ’yan gudun hijiran da yawansu ya haura mutum dubu 100 da suke watse a wurare daba-daban a ciki da wajen kasar nan.
Sanata Ndume ya ce galibin ’yan gudun hijirar mata ne da yara, kuma har yanzu gwamnati ba ta iya yin komai a kai ba, gashi sai ci gaba ake yi da kashe mutane. “Ina rokon gwamnati ta samar da kayan aiki ga sojojin Najeriya don su magance wannan matsala da ta addabe mu a cire batun siyasa da son zuciya a magance wannan matsala, domin sojan Najeriya sun fi dubu 100 kuma ’yan Boko Haram ba su wuce dubu 10 ba, to saboda me gwamnati ba za ta mayar da
hankali ta yaki wadannan ’yan ta’adda ba? A gaskiya talakawa suna cikin wahala, mu babu abin da za mu iya yi sai gwamnati, ga shi ga alama ba ta da niyyar yin komai kullum sai ci gaba abin yake yi ba kakkautawa, ana maganar siyasa da zaben 2015,” inji shi.
Ya ce mutanen jihohi uku da ke karkashin dokar ta-baci ba sa farin ciki da batun zaben saboda akasarinsu basa zaune a yankunansu.
Sanata Ndume ya ce ba ya tsammanin za a iya gudanar da zabe a jihohin uku, kuma idan aka ce za a yi wajibi ne Hukumar Zabe ta samar da yanayin da ’yan gudun hijira za su iya gudanar da zaben a inda suke gudun hijira, idan gwamnati ba za ta iya karbo garuruwan da ke hannun ’yan bindiga ba.