Sanata Ndume ya yi wa Majalisa bore

Sanata ya ki karbar sabon mukamin shugabanci da Majalisar Dattawa a nada shi

Sanata Ndume ya yi wa Majalisa bore

Sanata Ali Muhammad Ndume ya yi watsi da shugabancin da Majalisar Dattawa ta ba shi na kwamitin yawon bude ido.

Ndume ya yi wa nadin da aka bore ne yana mai cewa shi ba dan yawon bude ido ba ne.

Nadin da kuma boren na Ndume na zuwa ne kwanaki biyu bayan Majalisar Dattawan ta tsige shi daga kujerarsa ta Babban Mai Tsawatarwa.

A ranar Laraba ne shugabancin Jam’iyyarsa a majalisar ya maye gurbinsa da Sanata Tahir Mungono (Borno ta Arewa).

Aminiya ta ruwaito cewa dambarwar Ndume a Majalisar na da nasaba da sukan da ya yi wa kamun ludayin Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen magance matsalar yunwa da tsadar rayuwa a Najeriya.

A wata wasika da Shugaban Jam’iyya APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya aika wa majalisar, ya bukaci Ndume ya bar APC ya koma duk jam’iyyar adawar da ya zaba wa kansa.

Ganduje ya kuma bukaci a sauke Ndume daga mukaminsa na mai tsawatarwa, saboda abin da shugaban jam’iyyar ya kira kalaman da ba su dace ba da ke iya kawo wa shugaban kasar koma-baya.

Wannan lamari ya samo alsai ne daga hirar da dan majalisar ya yi da manema labarai inda a ciki ya koka cewa shugaban kasa bai san ainihin halin da al’umma suke ciki ba.

A cewarsa, wasu sun kange shugaban kasar daga yin magana a kan lamurra da kuma ganin jama’a, ballantana a samu yadda za a fayyace masa halin da jama’a suke ciki.

Dan majalisar ya kuma koka da cewa ’yan Najeriya sun riga sun yi fushi saboda yunwa da lalacewar yanayin karfin aljihunsu, ba tare da gwamnatin da dauki kwarararn matakan magance matsalolin ba.