Sanata Ningi ya dawo Majalisa bayan dakatarwar watanni uku
Da aka tambaye shi ko ya ji daɗin hutun nasa, Sanatan ya amsa da cewa: “Sosai kuwa.”
Ɗan majalisar da ke wakiltar Bauchi ta tsakiya, Sanata Abdul Ningi, ya dawo bakin aikinsa a zauren majalisar dattawa bayan dakatar da shi na tsawon watanni uku.
An dakatar da shi ne a watan Maris saboda iƙirarin cushen kuɗi.
- Katse lantarkin Najeriya: NLC da kamfanin TCN sun sa zare
- Tsohuwar matar wani alkali ta kashe shi a Kebbi
Amma a ranar Talata ne aka gano Ningi a harabar majalisar dokokin ƙasar da ke Abuja a cikin baƙar motarsa ƙirar Toyota Landcruiser Jeep.
Yana zuwa bakin kofar zauren Majalisar ya tsaya don yin musabaha da ’yan jarida da ke dakon zuwansa domin yi masa maraba.
“‘Yan jarida, na gode sosai,” ɗan majalisar cikin murmushi ya faɗa masu. “Na samu dukkan saƙonninku.”
Da aka tambaye shi ko ya ji daɗin hutun nasa, Sanatan ya amsa da cewa: “Sosai kuwa.”