Sanata Sankara na PDP ya koma APC

Alhaji Danladi Sankara, tsohon sanata mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso yamma ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar APC. Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru shi ne ya karbi Sankara a bikin da aka yi a filin Malam Aminu Kano da ke garin Dutse a ranar Lahadin da ta gabata. Badaru ya yi […]

Sanata Sankara na PDP ya koma APC

Alhaji Danladi Sankara, tsohon sanata mai wakiltar Jigawa ta Arewa maso yamma ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma jam’iyyar APC.
Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru shi ne ya karbi Sankara a bikin da aka yi a filin Malam Aminu Kano da ke garin Dutse a ranar Lahadin da ta gabata.
Badaru ya yi maraba da komawar sanatan cikin jam’iyyar APC inda ya ce komawarsa wani ci gaba ne a jam’iyyar a jihar.