Sanata Umar Kumo tsohon Sakataren jam’iyyar ANPP ya rasu

Ya rasu ya bar mata hudu, da ‘ya’ya 15 ciki har da jikoki.

Sanata Umar Kumo tsohon Sakataren jam’iyyar ANPP ya rasu

Tsohon Sakataren Jam’iyyar ANPP ta Kasa Sanata Sa’idu Umar Kumo ya rasu.

Ya rasu da safiyar Lahadi a asibitin Gwagwalada da ke Abuja, bayan gajeriyar rashin lafiya, yana da shekara 71.

Iyalansa sun shaida wa Aminiya cewa za a yi sallar jana’izarsa da misalin karfe 1 na rana a Babban Masallacin Kasa da ke Abuja.

Marigayi Sanata Kumo, ya wakilci Gombe ta Tsakiya a Majalisar Dattawan daga 1999 zuwa 2003.

An nada shi Sakataren rusasshiyar Jam’iyyar ANPP bayan faduwarsu babban zabe a 2007.

Daga baya kuma tsohon Shugaban Kasa, marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya nada shi Mataimakinsa na Musamman.

Kumo ya yi takarar Gwamnan Jihar Gombe a 2011, amma Ibrahim Hassan Dankwambo na jam’iyyar PDP ya kayar da shi.

A 2015 kuma ya zamo Daraktan-Janar na yakin neman zaben Dankwambo.

Kafin rasuwarsa, yana rike da sarautar gargajiya ta Garkuwar Gombe.

Sannan dan uwa ne ga tsohon Ministan Babban Birnin tarayya, Dakta Aliyu Umar Modibbo.

Ya rasu ya bar mata hudu, da ’ya’ya 15 da kuma jikoki.