Sanata ya raba tallafin awaki a Kaduna

Sanatan Arewacin Kaduna ya raba awaki 300 a matsayin tallafin dogaro da kai ga matan yankin

Sanata ya raba tallafin awaki a Kaduna

Akuya

Sanata Ibrahim Khalid Soba mai wakiltar Arewacin Kaduna ya raba awaki 300 a matsayin tallafin dogaro da kai ga matan yankin domin kara musu karfin aljihu.

Batun kiwon awaki na daga cikin abubuwan da jam’iyyar PDP ta mayar da hankali a kai a lokacin yakin namen zaben 2023, lamarin da ya ja mata zolaya daga APC da ke mulkin jihar.

Da yake jawabi a taron rabon awakin a Zariya, Sanata Khalid Soba ya ce kiwon dabbobin zai sama wa wadanda suka amfana abin da za su taimaka wa mazajensu.

“Awakin za su samar da kananan sana’o’i ga matan aure a yankunan karkara, musamman idan dabbobin suka fara haihuwa.

“Shi ya sa aka ba kowace mace awaki biyu da taure daya domin habaka yawan dabbobin nasu,” in ji shi.

An kuma ba su Naira dubu 10,o00 kowaccensu domin sayen abincin dabbobin.

A cewarsa, manonan rani 200 ma sun samu tallafin injinan ban ruwa a fadin kananan hukumomi takwas da yankuna 87 da ke mazabar sanatan.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos