Sanatan Amurka ya sake zargin Najeriya kan muzgunawa Kiristoci

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Cruz ya yi iƙirarin cewa, wasu manufofi da hukumomin Najeriya ke aiwatarwa sun taimaka wajen haifar da hare-hare kan Kiristoci

Sanatan Amurka ya sake zargin Najeriya kan muzgunawa Kiristoci

Sanatan Amurka Ted Cruz ya zargi gwamnatin Najeriya da mayar da hankali kan kamfen na kare martabarta a ƙasashen waje, maimakon magance zarge-zargen da ake yi na muzgunawa Kiristoci da sauran tsiraru masu addini.

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Cruz ya yi iƙirarin cewa, wasu manufofi da hukumomin Najeriya ke aiwatarwa sun taimaka wajen haifar da hare-hare kan Kiristoci da sauran tsiraru.

Ya ce, yana ci gaba da neman a qaqaba wa wasu jami’an Najeriya takunkumi saboda abin da ya kira take ’yancin addini.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta sha musanta waɗannan zarge-zarge, tana mai cewa, ba ta da hannu a muzgunawa mabiyan wani addini.

A baya gwamnatin ta ɗauki Kamfanin hulɗa da jama’a na Amurka domin bayyana matakan da take ɗauka wajen yaƙi da ta’addanci da kuma kare al’ummomin Kirista.

Rahotanni sun kuma nuna cewa, gwamnatin tarayya ta ware kuɗaɗe domin yaƙi da abin da ta kira yaɗa farfagandar da ke zargin Najeriya da muzgunawa Kiristoci.

Kuɗaɗen ajiyar Najeriya a waje sun ƙaru zuwa biliyan $52.73

Sanatan Amurka ya sake zargin Najeriya kan muzgunawa Kiristoci

2027: A guji tikitin Gwamna masu addini ɗaya — Sheikh Maraya

’Yan bindiga sun kai hari da kashe manoma 23