Sanatan Kaduna ya tsallake rijiya da baya

Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Usman Adamu, ya tsallake rijiya da baya a wani hari da ’yan ina-da-kisa suka kai masa.

Sanatan Kaduna ya tsallake rijiya da baya

Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Usman Adamu, ya tsallake rijiya da baya a wani hari da ’yan ina-da-kisa suka kai masa.

Sanatan, wanda aka fi sani da Mista La, ya sanar da haka ne a cikin dare, jim kaɗan bayan faruwar lamarin.

Daga da ƙarfe 10nma dare ranar Laraba ne Mista La ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa Allah Ya yi masa gyadar dogo bayan harin neman kashe shi da ka yi.

“Dazun nan ma tsallake rijiya da baya a wani harin neman kashe ni da aka yi a yankin Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa,” in ji Sanatan.

Sanarwar tasa ke da wuya mutane suka yin tsokaci a kai.

A yayin da wasu jajantawa da tashi murnar samu kuɓuwa, wasu kuma sun ƙara nuna damuwa kan taɓarɓarewar sha’anin tsaro.

Wasu kuma sun bayyana damuwa cewa idan har babban mutum kamarsa zai shiga irin wannan yanayi, to ina ga talaka.

Sanata Lawal Usman Adamu shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan ilimin bai-ɗaya a matakin farko.

’Yan bindiga sun sace Farfesa, sun nemi N10m kuɗin fansa

Za a ɗauke wutar lantarki na tsawon mako 2 a Abuja

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da Samha kan shigar banza

Sakataren Gwamnatin Ondo ya rasu bayan yin hatsarin mota