Sanatan Kano ya ba ’yan wasan kwallon hannu kyautar N2m Lakadan
Dan majalisar dattijai mai wakiltar Kano ta Arewa Sanata Barau I. Jibrin ya ba ’yan kungiyar wasan kwallon hannu na Kano Pillars da kuma ta mata Safety Babes, kyautar Naira Miliyan biyu Sanatan ya basu kyautar ne a bisa nasarar da su ka samu na lashe gasar cin kofin ‘Prudent Energy’ wanda aka gudanar a […]
Dan majalisar dattijai mai wakiltar Kano ta Arewa Sanata Barau I. Jibrin ya ba ’yan kungiyar wasan kwallon hannu na Kano Pillars da kuma ta mata Safety Babes, kyautar Naira Miliyan biyu
Sanatan ya basu kyautar ne a bisa nasarar da su ka samu na lashe gasar cin kofin ‘Prudent Energy’ wanda aka gudanar a jihar Legas a farkon watan Nuwamba.
Sanatan ya mika kyautar kudin ne lakadan ga Shugaban Hukumar Kula da Wasanni ta Jihar Kano, Ibrahim Galadima, a wani dan kwarya-kwaryar biki a ofishinsa a ranar Alhamis.
- Shugaban NFF ya je ta’aziyyar tsohon dan wasan Kano Pillars
- Ganduje ya sasanta da Barau, ya bar masa takarar Sanatan Kano ta Arewa
A jawabinsa yayin karbar kudin, Ibrahim Galadima ya yi godiya tare da jinjina wa Sanata Barau Jibrin bisa wannan karimci, da kuma cika alkawarin bayar da wannan kudin da ya yi a gaban gwamna.
A jawabin hadimin sanatan mai kula da tallafi da karfafar matasa, Hafizu Sani Liman Kofar Mata, wanda ya kai sakon kudin, ya kawo kudin ne a bisa alkawarin kyautar da sanatan ya yi.