Sanatanmu ya yi watsi da mu – Matasan Kano ta Arewa
Jagoran kungiyar Matasan Kano ta Arewa Malam Mustapha Umar Tallo Gwarzo ya yi zargin cewa Sanatan Mazabar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibirin ya yi watsi da su duk da irin fafutikar da suka yi domin ya zamo Sanatan mazabar.A tattaunawa da wakilinmu a karshen mako, Mustapha Tallo ya ce matasan yankin Kano ta Arewa […]
Jagoran kungiyar Matasan Kano ta Arewa Malam Mustapha Umar Tallo Gwarzo ya yi zargin cewa Sanatan Mazabar Kano ta Arewa, Sanata Barau Jibirin ya yi watsi da su duk da irin fafutikar da suka yi domin ya zamo Sanatan mazabar.
A tattaunawa da wakilinmu a karshen mako, Mustapha Tallo ya ce matasan yankin Kano ta Arewa sun ba da gagarumar gudummawa wajen ganin Sanata Barau Jibrin ya samu nasara a zaben bara, amma sai ga shi har yanzu bai waiwayi matasan ba, kuma hakan bai yi musu dadi ba.
Shugaban ya ce matasan yankin sun karade kananan hukumomin da ke mazabar tare da yin tarurruka da matasan yankin don tallata Sanata Barau Jibrin, amma abin mamaki har zuwa yanzu babu wata tuntuba a tsakaninsu balle su sanar da shi halin da mazabar tasa take ciki.
Ya ce bai kamata dan siyasa kamar Sanata Barau Jibrin bai ya nuna irin wannan hali ba, kuma yana da kyau ya san cewa akwai ranar bukatarsu tana nan dawowa, inda matasan za su sake duba wannan hali da suke ciki. Ya yi fatan cewa sauran zababbun da suka fito daga mazabar za su yi kokarin taimaka wa matasan yankin saboda matasa ne a sahun gaba wajen kawo canji a kowace kasa ta duniya.