Sanatoci na shirin tsige Ndume kan sukar Tinubu
Ana zargin magoya bayan Tinubu na yunkurin dakatar da Sanata Ali Ndume kan saukar Shugaba Tinubu kan yunwa da rashin tsaro
Sanatoci magoyon bayan Shugaba Tinubu na yunkurin tsige da Sanata Ali Muhammad Ndume saboda sukar da ya yi wa shugaban kasa kan yunwa da rashin tsaro da suka adabi ’yan Najeriya.
Majiyoyi a majalisar na cewa magoya bayan Tinubu na kuma shirin tsige shi daga kujerarsa ta mai tsawatarwar Majalisar Dattawa.
Yunkurin na zuwa ne watanni bayan majalisar ta dakatar da Sanata Abdul Ingila na watanni uku, saboda ya yi zargin cushen Naira tiriliyan 3.7 a kasafin kudin 2024, a yayin hirarsa da Sashen Hausa na BBC.
A lokacin wata hira da ’yan jarida a Majalisar Dattawa a makon jiya ne Ndume ya yi zargin cewa, Tinubu “ba shi da masaniya kan abubuwan da ke faruwa a wajen Fadar Shugaban Kasa.
- Kano: Abba ya sa hannu kan dokar karin masarautu uku
- A watan Agusta matatarmu za ta fara sayar da fetur —Dangote
“Wasu sun tare shi, yawancinmu kuma ba za mu iya bi ta bayan fage ba ballantana mu samu ganin shi.
“Yanzu sun ma hana shi yin magana a kan abubuwa, sannan ba shi da masu ba shi shawara kan al’amuran al’umma, sai kakakinsa, Ajuri Ngelale, da ke rubuta masa jawabi.
“’Yan Najeriya sun fusata; Gwamnati ba ta yin komai kan matsalar yunwa, wanda muka ke buƙatar a gaggauta daukar mataki.
“Ba mu da abinci a ajiye, akwai ƙarancin abinci, rashin abinci ne matsala mafi muni da za ta iya samun wata ƙasa.
“Karin munin lamarin shi ne haduwar wannan matsalar da ta tsaro.”
Wadannan kalaman ne suka ja wa Ndume suka daga wasu sanatocin jam’iyyarsa ta APC magoya bayan Tinubu.
Kan gaba a cacckar Ndume shi ne Sanata Sunday Karimi (Kogi West) da kuma APC.