Sanatoci sun fara muhawarar amincewa da karancin albashi
A yau Alhamis ne ‘yan majalisar dattawan Najeriya suke muhawarar amincewa da tsayar da Naira dubu 27 a matsayin karamin albashin ma’aikata a jihohi da Naira dubu 30 a matsayin karamin albashi ga ma’aikatan gwamnatin tarayya. An dai fara muhawarar ne bayan karban kudirin da Shugaba Buhari ya aikewa ‘yan majalisar don samun amincewar su. […]
Zauren Majalisar Dattawa
A yau Alhamis ne ‘yan majalisar dattawan Najeriya suke muhawarar amincewa da tsayar da Naira dubu 27 a matsayin karamin albashin ma’aikata a jihohi da Naira dubu 30 a matsayin karamin albashi ga ma’aikatan gwamnatin tarayya.
An dai fara muhawarar ne bayan karban kudirin da Shugaba Buhari ya aikewa ‘yan majalisar don samun amincewar su. Mataimakin shugaban majalisar dattawan Ike Ekweremadu ne ya karanta kudirin da shugaban Najeriya ya aika zauren majalisar.