Sanatoci sun halarci jana’izar sojojin da aka kashe a Delta

An yi jana’izar dakarun da suka sadaukar da rayukansu domin ƙasar nan a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba.

Sanatoci sun halarci jana’izar sojojin da aka kashe a Delta

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin a wurin jana’izar sojoji

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya jagoranci ‘yan Majalisar Tarayya wajen halartar jana’izar sojojin da aka kashe a Jihar Delta a ranar 14 ga watan Maris 2024.

An yi jana’izar dakarun da suka sadaukar da rayukansu domin ƙasar nan a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba.

Motocin bayar da agajin gaggawa na sojoji ne suka kai gawarwakinsu tare da rakiyar hukumar bayar da agajin gaggawa ta Birnin Tarayya.

‘Yan uwa da matan sojojin da suka rasa rayukansu sun halarci maƙabartar tare da matan abokan arziki.

Iyalan sojojin da aka kashe yayin halartar jana’izar a Abuja.
Wani sashe na ‘yan uwa da iyalan sojojin da aka kashe yayin halartar jana’izar a Abuja.
Gawarwakin sojojin da aka kashe yayin jana’izarsu a Abuja.