Sanatoci sun kusa ba hammata iska kan rikicin Jihar Ribas
A ranar Talatar da ta gabata ne Sanatoci suka yi yunkurin ba hammata iska sakamakon rikicin siyasar da ya dabaibaye Jihar Ribas. Sanatocin sun rika yi wa junansu bakaken maganganu har ta kai saura kadan su ba hammata iska. Al’amarin ya fara faru ne a lokacin da Sanata Wilson A. Ake (APC, Jihar Ribas) yake […]

A ranar Talatar da ta gabata ne Sanatoci suka yi yunkurin ba hammata iska sakamakon rikicin siyasar da ya dabaibaye Jihar Ribas.
Sanatocin sun rika yi wa junansu bakaken maganganu har ta kai saura kadan su ba hammata iska.
Al’amarin ya fara faru ne a lokacin da Sanata Wilson A. Ake (APC, Jihar Ribas) yake jawabi a kan yadda ‘yan sanda suka harbi Sanata Magnus Abe da harsashin roba a ranar 12 ga watan Janairu, 2014 a lokacin da ake taron siyasa a Fatakwal. A lokacin da yake jawabin ne sai sanatoci daga Jam’iyyar APC suka rika ihun nuna goyon bayansu gare shi, inda Sanata Ahmad Lawal (APC, daga Jihar Yobe) ya rika babatun sun mallaki kwararan hujjoji da ke nuna ruwan-da-tsakin ‘yan sandan Jihar Ribas cikin al’amarin. A nan ne sai Sanatocin Jam’iyyar PDP suka fara mayar da martani.
Bayan Sanata Ake ya kammala mika rubutaccen jawabinsa ne sai Sanata James Manager (PDP, daga Jihar Delta) ya kira Sanata Lawal ‘wawa’ ya ce “Kai wawa ne, yi mana shiru.”
Wannan sai ya kara rura wutar hamayyar inda sanatoci daga APC suka hasala, wanda ta sanya Sanata Lawan ya ce “Kai ne wawa, ya kamata ka ba da hakuri.” Daga nan ya fara yunkurin kama shi da kokawa.
Daga nan ne sai Sanata Jajere (APC, Jihar Yobe) ya mike daga kujerarsa sannan ya nufi wurin da Sanata Manager yake don su ba hammata iska, nan da nan sai Sanata Manager ya mike ya saurari isowarsa.
Hakan ta sanya aka shiga tsakani a wani bangare kuma suka ci gaba da fada wa juna bakaken maganganu.
dauki-ba-dadin ya faru na tsawon minti 15 ne. Bayan an shawo kan al’amarin ne, sai Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Dabid Mark ya yi alla-wadai da halin da ‘yan majalisun suka nuna, sannan ya bukaci su Sanata Lawan da Manager su yafe wa junansu.
Daga Majalisar ta amince a kan Sufeto-Janar na ’yan sandan Najeriya Mohammed dahiru Abubakar zai bayyana a gabanta don ya yi mata bayanin a kan rikicin Jihar Ribas.
Majalisar ta yi tir da yadda Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Ribas Mista Mbu ya ba da umarnin a harbi Sanata Magnus Abe da harsashin roba yayin taron siyasar da ya gudana a Fatakwal Jihar Ribas.