Sanatoci sun tabbatar da naɗin Shugabar Hukumar NFIU Hafsat Bakari
Hafsat Bakari lauya ce kuma kwararriya a fannin binciken harkokin kuɗi.
Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Hafsat Bakari a matsayin Shugabar Hukumar Kula da Hada-Hadar Kuɗi ta Najeriya wato NFIU.
Tabbatar da Hafsat a matsayin Shugabar NFIU ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin yaƙi da cin hanci da rashawa da ke karkashin jagorancin Sanata Emmanuel Udende Memga mai wakiltar mazabar Binuwai ta Arewa maso Gabas a majalisar.
- ’Yan takara sun bijire wa taron da Shugaba Macky Sall ya kira
- Akwai yiwuwar tsagaita wutar yaƙin Isra’ila a Gaza albarkacin watan Ramadana
A makon jiya ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Hafsat Bakari a matsayin Shugabar hukumar ta NFIU tare da miƙa wa Majalisar Dattawa domin tabbatar da ita.
A yayin fitar da sanarwa a kan naɗin Hafsat, mai magana da yawun Shugaban Tinubu, Mista Ajuri Ngelale ya ce Bakari lauya ce kuma kwararriya a fannin binciken harkokin kuɗi, wacce ta shafe shekaru da dama a fannin yaƙi da safarar kuɗaɗen haram, ɗaukan nauyin ta’addanci, da kuma yaki da cin hanci da rashawa.
A cewar Ngelale, kafin naɗin Shugabar Hukumar ta NFIU, ta taba zama Mataimakiyar Darakta a sashin kula da harkokin kuɗi na hukumar.
Haka kuma, ta kasance shugabar sashen kula da harkokin yau da kullum a lokuta daban-daban, baya ga shugabantar sashen tsare-tsaren dabaru da jagorantar sakatariyar kwamitin hukumar ta hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
Bayan naɗin ta, Shugaban Kasa na sa ran cewa, Hafsat Bakari za ta yi amfani da kwarewa da gogewarta wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta a wannan muhimmin aiki da aka bata.
Ana sa ran za ta ciri tuta musamman ganin yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ke ƙoƙarin yaƙi da masu safarar kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya, da sauran ayyukan aikata almundahana da kuɗaɗen al’umma da a halin yanzu ake gani a bangaren kasuwannin canjin kuɗaɗen waje na kasar nan, in ji Ngelale.