Sanatoci sun yi barazanar tsige Buhari

An samu hauragiya a Majalisar Dattawa a ranar Talatar da ta gabata, bayan da wani sanata ya kawo shawarar a tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari a wani zaman sirri da suka yi.Sanatocin da suka halarci zaman wanda aka yi cikin awa 1.15 ya shaida wa wakilinmu an kawo shawarar ce a lokacin da ake tattauna […]

Sanatoci sun yi barazanar tsige Buhari
Sanatoci sun yi barazanar tsige Buhari

An samu hauragiya a Majalisar Dattawa a ranar Talatar da ta gabata, bayan da wani sanata ya kawo shawarar a tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari a wani zaman sirri da suka yi.
Sanatocin da suka halarci zaman wanda aka yi cikin awa 1.15 ya shaida wa wakilinmu an kawo shawarar ce a lokacin da ake tattauna batun shari’ar jabun dokar majalisar da ake tuhumar Shugaba da Mataimakin Shugaban Maja;isar Sanata Bukola Saraki da Sanata Ike Ekweremadu da wadansu mutum biyu da hannu a ciki.
Bayanai sun ce Sanata Enyinnaya Abaribe (PDP, Abiya) ne ya kawo shawarar lokacin da Shugaban Kwamitin Shari’a, ’Yancin dan Adam da Harkokin Shari’a Sanata Dabid Umaru ya gabatar da rahoton kwamitinsa game da sammacin da aka aike wa Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana gaban majalisar kan shari’ar jabun dokokin majalisar.
Sanata Umaru ya shaida wa sanatocin cewa Malami ya ki amsa gayyatarsu.
“Wani sanata ya bayar da shawarar a sanya Sufeto Janar na ’Yan sanda Ibrahim K. Idris ya kama shi, amma wasu sanatoci suka ce ba zai iya aiwatar da umarnin ba saboda batun akwai hannun fadar Shugaban kasa a ciki,” wani sanata ya shaida wa wakilinmu.
Ya ce: “A daidai wannan lokaci ne Abaribe ya tashi ya ce, wajibi ne mu tunkari tushen batun. Da aka tambaye shi abin da yake nufi da tushen batun sai ya ce a fara bin hanyar yadda za a tsige Shugaban kasa.”
Ya ce sai wani sanata ya goyi bayansa wanda hakan ya harzuka sanatocin Jam’iyyar APC suka rika musayar munanan kalamai da takwaraorinsu na PDP, inda majiayrmu ta ce an shafe minti 30 ana hauragiya kafin Sanata Dabid Mark ya tsawatar.
Aminiya ba ta samu jin ta bakin Sanata Abaribe ba kan batun.
A dai wannan zama ne aka ce Sanata Dino Melaye (APC, Kogi ta Yamma) ya yi barazanar zai doki Sanata Oluremi Tinubu (APC, Lagas ta Tsakiya) wadda ta soki shawararsa ta a dakatar da sanatocin da suka kai kara kan jabun dokar majalisar.
An ruwaito Melaye yana cewa: “Tunda ba a shirye suke su janye karar ba, a dakatar da su kawai. Suna nan lokacin da aka yanke shawarar cewa littafin dokokin ba na jabu ba ne.”
Sai dai da aka tuntubi Melaye ya musanta cewa ya fada wa Sanata Tinubu maganganu marasa dadi a yayin muhawarar. “Na dai yi mata gargadi kan kiran sunana a bayaninta saboda a lokacin da na yi bayanina ban ambaci sunan kowa ba,” inji shi.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a shekaranjiya Laraba, Sanata Dino Melaye ya musanta labarin yunkurin tsige Shugaban kasar, inda ya ce babu wani yunkuri na tsige shi kan batun shari’ar ta su Bukola Saraki. Ya ce masu yada labaran ba su son zaman lafiyar Najeriya ne kawai.