Sandan girmar majalisar wakilai ta kara girma

Sabuwar dokar da Majalisar Wakilai ke aiki da ita, ta bai wa shugaban majalisar Yakubu Dogara karfin ikon ladabtar da daidaiku ko gungun mutanen da ke baradana ga kujerarsa. Ssababbin dokokin da aka fito da su na nuni da cewa sandar girma ta samu karin girma. Aminiya ta jiwo cewa, wannan al’amari ya auku ne […]

Sandan girmar majalisar wakilai ta kara girma
Sandan girmar majalisar wakilai ta kara girma

Sabuwar dokar da Majalisar Wakilai ke aiki da ita, ta bai wa shugaban majalisar Yakubu Dogara karfin ikon ladabtar da daidaiku ko gungun mutanen da ke baradana ga kujerarsa. Ssababbin dokokin da aka fito da su na nuni da cewa sandar girma ta samu karin girma.

Aminiya ta jiwo cewa, wannan al’amari ya auku ne a sanadiyyar kasancewar Dogara shugaban majalisar tun daga 9 ga Yunin bana. Ya ci karo da bukatar jam’iyyarsa ta APC, shi ya sa ya jajicre wajen tabbatar da karfin ikonsa wajen jan ragamar majalisar.
Sabuwar dokar an amince da ita ne a ranar 8 ga Oktobar bana, bisa la’akari da rahoton kwamitin musamman mai mutum 15 a karkashjin jagorancin dan majaisa shagari, wanda aka dora wa alhakin bibiyar dokoki da ayyukan majalisar da ya yi nazarin tsayayyen umarnin majalisar.
Don haka kwmaitin ya bijiro da cewa, wani dan majalisar “da ya tunkari sandar girma da kowace irin manufa” a lokacin da aka shiga rudani, to za a dakatrar da shi/ita na tsawon watanni shida.
Sabuwar dokar ta bijiro da cewa: “Sandar girma ita ce karfin ikon majalisar, saboda haka sai ma’aikacin da aka umarta, wato jami’in tsaron da ke dakonta zai iya tunkararta, ko ajiyeta ko daukarta a lokacin gudanar da aikin jami’in
Sannan akwai wata dokjara ta 112 (8) da ta ce: Majalisa da kwamitocinta za su dage tsayin daka wajen bin ka’idoji da tsare-tsaren da aka gindaya musu wajen aiwatar da ayyukansu, wanda ya hada da kundin sa’ido da tantancewa da kundin dokokin kwamit da kundin rahotanni da kundin sauraren koken al’umma.
Wasu daga cikin ’yan majalisar sun bnayyana wa Aminiya cewa sababbin dokokin sun kara wa shugaban majalisar karfin ikon da yake bukata, don shawo kan ’yan adawa, wadanda ke da burin ganin sun tsige shi.
Dangane da dokar dakatar da mutum har tsawon zaman kwanaki 30, wani dan majalisa ya ce: “Mun zabi shugaba, muina girmama shi. Idan ya ce ka zauna ko yanke dokar fitar da kai, dole ka yi biyayya. Mun aiwatar da komai bisa la’akari da manufofin kafa dokoki don yi wa mutanen Najeriya aiki, don haka ba ma bukatar wani ya yi mana katsalandan wajen gudanar da ayyukan mu.”