Sandar Majalisa ta yi layar zana a Ogun
Wasu miyagu sun fasa zauren Majalisar Dokokin Jihar Ogun sannan suka yi awon gaba da sandar ikon majalisar. Da tsakar dare ne mutanen da ba a san ko su waye ba suka fasa Ofishin Shugaban Majalisar, Olakunle Oluomo, suka arce da sandar majalisar. An rage farashin Data da kashi 50 a 2020 a Najeriya Badakalar […]
Wasu miyagu sun fasa zauren Majalisar Dokokin Jihar Ogun sannan suka yi awon gaba da sandar ikon majalisar.
Da tsakar dare ne mutanen da ba a san ko su waye ba suka fasa Ofishin Shugaban Majalisar, Olakunle Oluomo, suka arce da sandar majalisar.
“Tabbas wani abin takaici ya faru a majalisar inda bata-gari suka shiga ta cikin silin suka dauke sandar ikon majalisar”, inji kakarin Rundunar ’Yan Sandan jihar, Abimbola Oyeyemi yayin da yake tabbatar da aukuwar lamarin.
Wakilin Aminiya ta ziyarci majalisar domin ganin halin da aka ciki amma jami’an tsaro ba su bari ya shiga ba, saboda umarnin da suka ce an ba su.
“Akawun Majalisa ya ba da umarni cewa kar a bar ’yan jarida su shiga.
“Kun saba shiga ba tare da matsala ba, amma yau an ba mu umarni kar mu bari kowa ya shiga harabar”, kamar yadda wani jami’in NSCDC ya shaida wa wakilinmu.
Aminiya ta gano cea Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Edward Ajogun ya ziyarci majalisar ranar Alhamis.
Da yake wa Aminiya karin bayani, kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya ce an gano sandar majalisar kuma an fara binciken faruwar lamarin.