Sani Danja ya yi sabuwar waka da Terry G
Fitaccen jarumi kuma mawakin fina-finan Hausa Sani Danja ya yi sabuwar waka da mawakin Hip Hop din Najeriya Terry G.Taken wakar shi ne, ‘Ba Su Iyawa’, tana da tsawon minti 3 da sakan 26. Kamfanin Danja Records da Sanusi Montage 7Hills suka daukin nauyin wakar. Terry G ne ya ba da umarni.An yi wakar ne […]

Fitaccen jarumi kuma mawakin fina-finan Hausa Sani Danja ya yi sabuwar waka da mawakin Hip Hop din Najeriya Terry G.
Taken wakar shi ne, ‘Ba Su Iyawa’, tana da tsawon minti 3 da sakan 26.
Kamfanin Danja Records da Sanusi Montage 7Hills suka daukin nauyin wakar. Terry G ne ya ba da umarni.
An yi wakar ne da harsuna uku da suka hada da Hausa da Yarabanci da kuma Turancin Pidgin.
An nuno Sani Danja da kuma Terry G sanye babbar riga, inda Terry G yake rike da kararrawa kamar yadda ya saba rikewa a yayin da yake gudanar da daukar bidiyon wakokinsa.
A wakar an nuno Sani Danja na yi wa kansa kirarin cewa mahassadansa sun zama kamar kyanwar Lami da ba ta cizo, ba ta yakushi, ba ta kama bera, sai dai kuka.
Ya ce ba za su iya ja da shi ba, a bangaren kudi da rawa da juyi da ’yan mata da kuma iya sanya tufafi, daga nan aka nuno su sanye da kwat suna cashewa tsanakin ’yan mata.
Aminiya ta ji ta bakin Sani Danja inda ya ce, makasudin wakar shi ne don hada kan ’yan Najeriya ba tare da bambanta yare ko kabila ko addini ba, shi ya sa ma aka yi wakar da Hausa da Yarabanci da kuma Turancin Pidgin.