Sani Danja ya yi sabuwar waka mai taken ‘Alhaji’

Fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa Sani Musa Danja ya fitar da sabuwar wakarsa mai taken ‘Alhaji’.Mawakin ya sanya wakar tasa mai tsawon minti 4 da sakan 2 a shafinsa na twitter da kuma na intanet.Ya yi wakar da Hausa da Turancin Pidgin da kuma Yarabanci.Ya ce wakar ta shafi rayuwarsa ne, ya yi ta […]

Sani Danja ya yi sabuwar waka mai taken ‘Alhaji’
Sani Danja ya yi sabuwar waka mai taken ‘Alhaji’

Fitaccen mawaki kuma jarumin fina-finan Hausa Sani Musa Danja ya fitar da sabuwar wakarsa mai taken ‘Alhaji’.
Mawakin ya sanya wakar tasa mai tsawon minti 4 da sakan 2 a shafinsa na twitter da kuma na intanet.
Ya yi wakar da Hausa da Turancin Pidgin da kuma Yarabanci.
Ya ce wakar ta shafi rayuwarsa ne, ya yi ta ne don tuna wa mutane tambayar da suke yi wane ne kuma Sani Danja idan an sa sunansa a cikin jerin mawakan da za su yi waka yayin galar barkwanci a Kudancin Najeriya; galar da ake kira da Turanci Night of Thousand Laugh. Amma a yanzu jama’a tun daga Kano zuwa Legas suna kiransa da Alhaji. Ya ce sauran kasashen waje ma Alhaji suke kiransa.
Ya zuga kansa a wakar inda ya ce ya zama babban yaro, gwani ne shi wajen iya rawa da waka, yana kuma so mutane su sani yana da ’yan mata buhun-buhu.
A yanzu dai mawakin ya yi waka da Terry G da bector da White Nigerian da biper da sauransu. Tauraruwarsa tana haskakawa a Kudancin Najeriya.