Sani Gazas Chinade, Damaturu
Rundunar dawo da zaman lafiya (JTF) a Jihar Yobe ta ce ta halaka wasu ’yan bindiga da ake zaton ’ya’yan kungiyar Jam’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ne kuma ta damke wasu daga cikinsu hade da miyagun makamai masu yawa a wani samame da ta kai a […]
Rundunar dawo da zaman lafiya (JTF) a Jihar Yobe ta ce ta halaka wasu ’yan bindiga da ake zaton ’ya’yan kungiyar Jam’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ne kuma ta damke wasu daga cikinsu hade da miyagun makamai masu yawa a wani samame da ta kai a tungarsu da ke dajin Mnawachi da Abakire a karamar Hukumar Fune.
Samamen na JTF ya biyo bayan harin da ake zargin ’ya’yan kungiyar da kaiwa ga jami’an JTF a shingen duba abubuwan hawa da ke gab da garin Dogon Kuka a karamar Hukumar Fune ce a ranar Alhamis din makon jiya, inda ’yan bindigar suka arce da motar ’yan sanda dauke da kayan aiki zuwa Maiduguri.
Kakakin JTF a Jihar Yobe Laftana Eli Lazarus wanda ya nuna kayayyakin ga manema labarai a Damaturu, ya tabbatar da kai hari a shingen, inda ya ce a gumurzun da suka yi da ’yan bindigar, sun halaka wasu da ji wa da dama raunuka tare da cafke wasu, yayin da suka kwato miyagun makaman da suka hada da bindiga kirar AK 47 daya da roka guda uku da bama-bamai da caja mai lakanin RPG 3, sai sundukan alburusai guda 485.
Sauran a cewarsa, sun hada da riguna masu sulke na ’yan sanda guda 42 da hulunan kwano na ’yan sanda guda 44 da sundukan harsashin bindiga AK 47 guda 6 da wukake sama da 80 da mota daya da motar ’yan sandan da suka tsere da ita da magunguna da wasu kayayyakin amfanin yau da kullum.
Ya nemi jama’a su rika kai rahoto cikin sauri ga rundunar da zarar sun gano mutanen da ke da alamar rashin gaskiya don daukar mataki kafin su aikata miyagun ayyuka.