Sani Gazas Chinade, Damaturu

Aminiya: Me za ka ce game da shekara 16 na mulkin PDP a Jihar Bauchi?Mai’auduga: Dukkan godiya ya tabbata ga Allah Madaukacin Sarki. Kamar yadda kowa ya sani ne Allah ke ba da mulki ga wanda Ya so. Jam’iyyar PDP ta shafe shekara 16 tana mulki a Bauchi kowa ya ga kamun ludayinta yanzu kuma […]

Sani Gazas Chinade, Damaturu
Sani Gazas Chinade, Damaturu

Aminiya: Me za ka ce game da shekara 16 na mulkin PDP a Jihar Bauchi?
Mai’auduga: Dukkan godiya ya tabbata ga Allah Madaukacin Sarki. Kamar yadda kowa ya sani ne Allah ke ba da mulki ga wanda Ya so. Jam’iyyar PDP ta shafe shekara 16 tana mulki a Bauchi kowa ya ga kamun ludayinta yanzu kuma APC ce ke rike da ragamar shugabanci tun daga matakin jiha har zuwa Gwamnatin Tarayya.
Saboda haka jihohi da dama na Najeriya gwamnonin APC ne suke gudanar da mulki, amma babban abin da yake faranta min rai shi ne an fara samun zaman lafiya a tsakanin al’umma kusan kowa ya samu natsuwa a jikinsa, muna godiya ga Allah bisa wannan nasara.
Kafin zaben Shugaban kasa da na gwamnoni da ’yan Majalisar Tarayya da sanatoci kusan kowa hankalinsa a tashe yake domin ’yan bindiga sun addabi yankin Arewa maso Gabas wanda ya yi sanadiyar hallaka dimbin rayukan jama’a.
Aminiya: Tsakanin ’yan siyasar Arewa da na Kudu su wa suka fi aiki ga talakawansu?
Mai’auduga: Kafin in ba da amsar wannan tambaya sai mun koma baya domin akwai matasa da dama wadanda ba su da tarihin abubuwan da suka faru a shekarun baya, misali lokacin da aka hada Kudu da Arewa a 1914.  Hakika babu ’yan siyasar da suka fi sukar shugabanninsu kamar ’yan Arewa, lokacin da mutum yake shugabanci ya fi kowa bakin jini. Da zarar ka sauka daga mulki sai ka ji mutane suna fadin abubuwan alheri da mutum ya yi. Shugabannin Kudu da zarar sun karbi kudi daga Asusun Tarayya sai su zauna su raba a tsakaninsu da sarakunan yankin, babu wani aikin raya kasa da suke gudanarwa ga mutanensu. Misali lokacin da tsohon Gwamna Ahmadu Adamu Mu’azu yake mulki a Jihar Bauchi ya sha suka daga sassa daban-daban haka kuma lokacin da Malam Isa Yuguda yake mulki ya sha suka iri-iri amma yanzu da za ka kewaya cikin fadar jiha babu dan siyasar da yake da farin jini kamar Malam Isa Yuguda. Don haka maganar gaskiya ita ce ’yan siyasar Arewa suna matukar kokari amma ba a fadin alherinsu sai bayan sun sauka daga mulki.
Aminiya: Wane hali jam’iyyarku ta PDP take ciki a Jihar Bauchi?
Mai’auduga: Jam’iyyar PDP tana nan lami lafiya a Jihar Bauchi kuma yanzu haka mun fara shirye-shiryen kwace mulki a zaben shekara ta 2019, domin yanzu mutane sun fara ganin alherin mulkin PDP a Bauchi. Ina so a fahimci cewa mutanen Jihar Bauchi Buhari suka zaba ba Jam’iyyar APC ba, domin da yawa daga cikin wadanda suke cikin APC a Bauchi daga jam’iyyarmu ta PDP suka fito tun daga kan Gwamnan har zuwa kasa domin ya nemi takarar Sanata a karkashin PDP a shiyyar Bauchi ta Kudu a baya.
Aminiya: Kana ganin PDP za ta sake kafa gwamnati a Jihar Bauchi?
Mai’auduga: Ina tabbatar maka cewa ko gobe aka sa akwatin zabe a Jihar Bauchi PDP, za ta kafa gwamnati domin mutane sun fara fahimtar gaskiya, amma Shugaban kasa Muhammadu Buhari mun gamsu da yadda yake tafiyar da Najeriya.
Aminiya: Mene ne gaskiyar batun da ke cewa dan takarar Shugaban kasa na PDP a zaben 2019 zai fito daga Arewa maso Gabas ne?
Mai’auduga: Tabbas PDP ta shiga cikin mawuyacin hali, amma yanzu abubuwa za su gyaru tunda an gano bakin zaren, ina daya daga cikin wadanda suke goyon bayan dan takarar Shugaban kasa na PDP ya fito daga shiyyar Arewa maso Gabas. Kuma a ra’ayina na fi so ya fito daga Jihar Bauchi don haka muna fatar Allah Ya zaba mana abin da ya fi alheri. Sama da kashi 85 cikin 100 na magoya bayan PDP suna son dan takarar Shugaban kasa a zaben shekara ta 2019 ya fito daga shiyyar Arewa maso Gabas domin mu ne ba mu taba yin shugabancin kasar nan ba.
Aminiya: Mene ne sakonka ga magoya bayan PDP da suke ganin ba za su rayu ba sai da gwamnati?
Mai’auduga: Abin da zan fada wa magoya bayan PDP da sauran al’umma baki daya shi ne kowa ya kama sana’a, kuma duk wanda yake son shiga siyasa ya nemi abin yi domin ta haka ne zai rike akidarsa ta gaskiya. Bayan haka sai mutane sun cire kwadayinsu a kan gwamnati, babu wata al’umma da za ta samu ci gaba mai amfani sai kowa yana da hanyar dogaro da kai.
Aminiya: A karshe mene ne sakonka ga jama’a?
Mai’auduga: Babban sakona ga al’umma shi ne kowa ya yi hakuri da rayuwa, shugabanni kuma a ci gaba da yi musu addu’o’i domin ta haka ne za su samu damar cika alkawuran da suka dauka a lokacin kamfen.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sababbin ministocinsa muna yi musu fatar alheri amma tabbas PDP za ta kwace kujerar Gwamnan Jihar Bauchi a zaben 2019.