Sani Lulu ya dauki nauyin ’yan kwallo 14 don karo ilimi

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) Alhaji Sani Lulu Abdullahi ya dauki nauyin kimanin matasan ’yan kwallo 14 daga sassan kasar nan don karo ilimi a Kwalejin POSLA Academy da ke Karshi a Abuja.A lokacin da yake sanar da haka a ranar Litinin da ta wuce a Abuja, Alhaji Sani Lulu wanda kuma […]

Sani Lulu ya dauki nauyin ’yan kwallo 14 don karo ilimi
Sani Lulu ya dauki nauyin ’yan kwallo 14 don karo ilimi

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) Alhaji Sani Lulu Abdullahi ya dauki nauyin kimanin matasan ’yan kwallo 14 daga sassan kasar nan don karo ilimi a Kwalejin POSLA Academy da ke Karshi a Abuja.
A lokacin da yake sanar da haka a ranar Litinin da ta wuce a Abuja, Alhaji Sani Lulu wanda kuma shi ne Daraktan Wasanni na Ma’aikatar kula da Babban Birnin Tarayya, Abuja (FCT), ya ce wadanda suka samu wannan tallafi sun hada da maza 10 da mata hudu wadanda za su fara yin karatu daga zangon karatu mai zuwa.
Ya ce kimanin Naira miliyan 10 ya ware wajen daukar dawainiyar karatunsu a wannan makaranta.
“Muna gudanar da wannan gasa ce a duk shekara wajen zakulo matasan ’yan kwallo a bangaren maza da na mata don ba su gurbin karo karatu a Kwalejin POSLA da ke Karshi a garin Abuja kuma za  su cigaba da gudanar da wasan kwallon kafa a yayin karatunsu ba tare da matsala ba”.
“Wadannan matasa sun samu nasara ne daga cikin matasa kimanin 50 da muka tattara don yi musu gwaji”.
An zabo wadannan matasa ne a wata gasar kwallon kafa da Sani Lulu ya shirya  a Jihar Kogi da kuma a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda aka gudanar da wasan karshe a Abuja.  Hakan ta ba matasan damar yin jarrabawar share fagen shiga Kwalejin POSLA Academy da aka fi sani da (Common Entrance Edamination) inda aka dauki goman farko a bangaren maza yayin da aka zabi hudun farko daga bangaren mata.
Kimanin Naira miliyan 10 ne Alhaji Sani Lulu ya ware wajen daukar nauyin wadannan matasa a Kwalejin POSLA da ke Abuja, inda baya ga yin karatu za su cigaba da gudanar da wasan kwallon kafa.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa