Sani Rainbow: Kannywood ta kusa zama tarihi saboda satar fasaha

Alhaji Sani Abubakar wanda aka fi sani da lakabin Sani Rainbow shi ne babban dillalin fina-finan Hausa, ya yi bayanin dalilin da ya sa ya fara kasuwancin fina-finan Hausa da kuma matsalolin da yake fuskanta a harkar. Ya ce masana’antar fim na gab da durkushewa dalilin satar fasaha. Za mu fara da tarihinka…Assalamu alaikum, sunana […]

Sani Rainbow: Kannywood ta kusa zama tarihi saboda satar fasaha
Sani Rainbow: Kannywood ta kusa zama tarihi saboda satar fasaha

Alhaji Sani Abubakar wanda aka fi sani da lakabin Sani Rainbow shi ne babban dillalin fina-finan Hausa, ya yi bayanin dalilin da ya sa ya fara kasuwancin fina-finan Hausa da kuma matsalolin da yake fuskanta a harkar. Ya ce masana’antar fim na gab da durkushewa dalilin satar fasaha.

Za mu fara da tarihinka…
Assalamu alaikum, sunana Alhaji Sani Abubakar, amma ana yi mini lakabi da Sani Rainbow.  Na samu lkabin ne daga kamfanina na Rainbow CD, wanda ke kasuwanci da kuma shirya fina-finan Hausa. An haife ni a garin Gusau Jihar Zamfara. Na yi Model Primary School da ke Kanwuri, Gusau, Jihar Zamfara. Na yi makarantar Islamiyya ta Hisbuz Rahim da ke garin Gusau. Na yi makarantar sakandare da ake kira Sambo Secondary School a garin Gusau. Daga nan na yi Difloma a kwas din Public Administration a Federal Polytechnic da ke Bauchi.
Bayan na dawo Gasau har na fara kasuwanci, sai na sake koma wa Federal Polytechnic Kauran Namoda na yi HND a kwas din Business Administration. Na yi hidimar kasa a Jihar Oyo. Bayan na kammala hidimar kasa ban yi aikin gwamnati ba sai na ci gaba da kasuwanci gadan-gadan.  
Na fara kasuwancin ne a bangare fina-finan Hausa, wato wanda ake kira bideo Club. Na ci gaba da harkar wanda a yanzu nake da babban kamfanin kasuwanci da kuma shirya fina-finai.

Ga shi ka yi karatu mai zurfi kuma ba ka nemi aikin gwamnati kamar yadda yawancin wadanda suka yi karatu suke yi ba, sai ka fara harkar fina-finai, ko me ya jawo hakan?
Kamar yadda na fada maka a baya ne, na yi HND dina a kwas din da ya shafi harkokin kasuwanci (Business Administration), bayan na kammala hidimar kasa sai na rika tunanin abin da zan yi in dogara da kaina, saboda lokacin da nake makaranta wani lakcaranmu ya yi mana bayani mai kama jiki kan duk wanda ya karanta sashin kasuwanci, to ba dole sai yi aikin gwamnati ba, ya ce sashin kasuwanci yana da wani matsayi da ya bambanta da sauran nau’ikan karatu kamar aikin Injiniya da Likita da sauransu, kasancewar wadannan kwasa-kwasai yawanci sukan jingina da wani bangare ne kamar ma’aikata ko kamfani da sauransu. Don haka wanda ya karanta sashin kasuwanci ya san yadda zai juya kudi kalilan har a samu riba. Bayaninsa ya yi tasiri a kaina.
Sannan dan kasuwa zai koya wa wani, kuma jama’a da dama za su karu da shi. Daga nan na zabi bangare masana’antar shirya fina-finan Hausa, duk da cewa daga baya na bunkasa kamfani zuwa sauran harkokin kasuwanci daban-daban, amma da yake bangaren Kannywood ya fi suna da kuma daukar hankalin jama’a, sai ya kasance ta nan aka san mu.
Da yaya ka fara harkar kasuwancin fina-finan Hausa?
Tabbas na fara harkar fim tun daga kasa, na san dadinta da kuma wuyarta, kodayake na fara harkar ne a cikin dadi, saboda a lokacin ana kaset din bidiyo ne, ina yi maka maganar 1999 ke nan, lokacin da muka bude shagonmu mai suna Rainbow bideo Centre a garin Gusau, a lokacin jiranmu ake mu kawo fina-finai daga Kano, fina-finai irinsu ‘Wasila’ da ‘Sangaya’ da sauransu. Har layi ake yi mana, lokacin sana’ar tana da kima da kuma daraja, mun ci gaba a haka har zuwa lokacin da aka daina yayin bidiyo kaset, wato aka koma bCD, a hankali kamfanin ya bunkasa har aka samu rassa a Kano da Legas da Kaduna da sauransu.
A lokacin da ka fara harkar kasuwancin fina-finan Hausa wadanne matsaloli ka fuskanta, sannan ta yaya ka shawo kansu har zuwa yanzu ake damawa da ku a harkar?
Ka san na fara harkar cikin dadi, amma babbar matsalar da na fuskanta shi ne lokacin da na yi kokarin canza bCD zuwa DbD, wannan kuwa ya faru ne lokacin fina-finanmu masu suna ‘dan Marayan Zaki’ da kuma ‘karangiya’, mun je Legas muka bincika kamfanin da suke buga mana faya-fayan bCD, sai muka bukaci su buga mana faya-fayan bCD, sai suka ce mana ba sa bugawa. Hakan ya sanya muka yanke shawarar zuwa China don a bugo fim din ‘dan Marayan Zaki’, mun je China, amma cikin rashin sa’a, sai muka hadu da mayaudara, mun samu matsaloli sosai. Aikin bai yi kyawu ba, mun yi asarar kudi mai yawa. An kawo kayan gida, amma duka ba su yi aiki a Najeriya ba. Hakan ya sa muka sake buga su a faifan bCD.
Wane abu na farin ciki kake ji idan aka ambaci harkar fim?
Nakan ji farin ciki ne idan na duba irin mutanen da suke cin abinci a karkashin sana’ar fim. Tun daga masu rike fitila da kwalliya da samar da wurin daukar fim da sauransu. Za ka ga kowa cikin rufin asiri. Harka ce da mutane da yawa ke amfana.
Wadanne nasarori ka cim ma a harkar fim?
Nasarorin suna da yawa, sai dai mu kara godiya ga Allah. Tun lokacin da kamfaninmu na Rainbow CD ya fara kasuwanci fim dinsa na farko mai suna ‘Garinmu Da Zafi’, wanda muka sayi hakkin mallaka daga Kamfanin UK Entertainment,  yau shekara 8 zuwa 9 ke nan, to kodayaushe masu kallo suna jiran fim dinmu, domin sun san ba za mu kawo musu fim din banza ba. Ka ga wannan babbar nasara ce, saboda ba mu taba bata wa ’yan fim rai ba. Jama’a suna yaba wa fina-finanmu. Jira ake mu fitar da fim, ko kuma ka ji ana tambayar yaushe za mu fitar da fim. Ko da kasuwa ta tsaya, idan muka fitar da fim sai ka ga ta motsa. Misali a yanzu kasuwa ta tsaya, amma muna fitar da fim din ‘Namaliya’ ya sa ta fara motsawa.
A yanzu wadanne matsaloli ne suka damu harkar fim musamman ma bangaren kasuwanci?
Tun da aka fara harkar fina-finan Hausa ba mu taba samun kanmu cikin matsalar da muka samu kanmu a ciki yanzu ba. A halin da ake ciki harkar fim ta kusa zama tarihi, saboda masu satar fasaha, a da idan ka kashe miliyan 10 a fim, aka kawo shi kasuwa sai ka samu ribar da za ta nunnuka kudin da ka kashe. Hakan ya ba mu kwarin gwiwar sake koma wa lokeshin don daukar wani fim din. Yanzu halin ake ciki ya kai idan ka kashe miliyan 5 ka yi fim ka kai kasuwa, sai ya zama ba ka sayar da na Naira miliyan 1 ba, amma masu satar fasaha sun fara sayar da shi, idan kana sayar da shi a kan Naira 150 sai su sayar da shi Naira 80. Jama’a sai suka bi araha. Satar fasaha ta addabi kasuwa, ta sanya ba a mayar da uwar kudi, ballantana riba.
Za mu ci gaba in sha Allah