Sani Toro ya koka kan yawan shan kwayoyi a tsakanin matasan Bauchi
Tsohon Babban Sakataren Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFA) kuma Shugaban Jam’iyyar PDP a shiyyar Bauchi ta Kudu, Alhaji Sani Ahmad Toro ya bayyana damuwa kan yadda wadansu daga cikin matasan jihar suke ci gaba da tu’ammali da miyagun kwayoyi, inda ya ce babu wata al’umma da za ta samu ci gaba da bunkasar tattalin […]
Tsohon Babban Sakataren Hukumar kwallon kafa ta kasa (NFA) kuma Shugaban Jam’iyyar PDP a shiyyar Bauchi ta Kudu, Alhaji Sani Ahmad Toro ya bayyana damuwa kan yadda wadansu daga cikin matasan jihar suke ci gaba da tu’ammali da miyagun kwayoyi, inda ya ce babu wata al’umma da za ta samu ci gaba da bunkasar tattalin arzikin kasa a ya yin da matasanta suke ci gaba da shaye-shaye.
Alhaji Sani Toro ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilinmu a Bauchi inda ya ce “Matasa da dama sun lalace sakamakon shan kwayoyi, akwai wadanda suke ganin talauci da rashin aikin yi ne daya daga cikin abubuwan da ke sa matasan shan kwayoyi domin huce takaici. Ya kamata gwamnati ta dage sosai domin magance matsalar rashin aiki yi a tsakanin matasa, Najeriya za ta wargaje matukar wannan matsala ta ci gaba,” inji shi.
Alhaji Sani Toro ya ce akwai lokacin da ya ga wadansu matasa masu yawa a kofar shagon wani dan kabilar Ibo, inda ya isa kofar shagon sai ya ga matasan kowa da kwalba a hannunsa yana shan miyagun kwayoyi, ya ce wannan abu ya daga masa hankali sosai.
“Don haka matukar ba a magance wannan matsala ba, to tabbas za mu shiga cikin mummunan hadari a nan gaba. Don haka muna ba da shawara ga limamai da shugabannin coci-coci da sauran masu ruwa da tsaki kowa ya ba da tasa gudunmawa domin magance wannan matsala da ke neman zamowa ruwan dare,” inji Sani Toro.
Alhaji Sani toro ya bukaci hukumomin yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi da jami’an tsaro su bullo da sababbin dabaru na hukunta masu safarar kwayoyin, inda ya ce duk lokacin da aka magance masu sayarwa to masu sha za su yi karanci. “Ya kamata a rika binciken shagunan da suke sayar da magunguna, matukar gwamnati ta yi haka matsalar za ta ragu ko ta zamo tarihi a jihar da Najeriya baki daya,” inji shi.